✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sheikh Ibrahim Khalil ya sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC

Shugaban jam'iyyar ADC na Kano ne ya tabbatar da sauya shekar fitaccen malamin.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulkin jihar zuwa jam’iyyar ADC.

Sheikh Khalil ya sauya sheka ne tare da Dokta Saidu Ahmad Dukawa, kamar yadda Shugaban Jam’iyyar ADC Reshen Jihar Kano, Musa Shuaibu Ungogo, ya tabbatar wa manema labarai.

Shugaban jam’iyyar, ya bayyana cewa Sheikh Khalil ya sauya sheka tare da wasu farfesoshi takwas, don ceto Jihar Kano daga rashin shugabanci na gari, shan miyagun kwayoyi da kuma barace-barace.

Ungogo ya kara da cewa nan ba da jimawa ba uwar jam’iyyar ta ADC za ta shirya wa sabbin wadanda suka sauya shekar biki na musamman don murnar karbarsu zuwa jam’iyyar.

Sheikh Khalil ya sauya sheka daga APC zuwa ADC sakamakon yadda al’amura ke ci gaba da kamari a jam’iyyar.