Rasuwar fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Abubakar Giro Argungu babban rashi ne ga al’ummar Musumlin duniya baki daya, a cewar Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Jihar Gombe.
Gwamnan ya bayyana kaduwarsa da rasuwar Sheikh Giro Argungu, wanda ya bayyana a masayin malami abin koyi da yake yada fatawa ta hanyar sunnar Annabi Muhammad (SAW) ba tare da jawo fitina ba.
- Ya harbi angon wadda ta ki auren sa ana tsaka da biki
- NAJERIYA A YAU: Bambancin Kotun Zaɓen 2023 Da Na Baya
“Rayuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu abun koyi ce domin ya sadaukar da kan sa wajen koyar da addini Islama da Kuma koyar da hakuri da wanzar da zaman lafiya.” Inji gwamnan.
Da yake mika ta’aziyyarsa da ma daukacin al’ummar Jihar Gombe ga iyalan Sheikh Giro, Gwamnan Inuwa, ya ce yaba da gagarumar gudummawar shehin malamin wajen yada da’awar Musulunci, wanda ya ce rasuwarsa ta haifar da wawakeken gibi mai wuyar cikewa a bangaren.
Inuwa wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, ya kuma jajanta wa kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) inda Sheik Giro Argungu ya bada gudumawa sosai wajen ci gaban addini.
Sakon ta’aziyar, dauke da sa hannun kakakin gidan gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya yi wa Gwamnatin Jihar Kebbi da daukacin al’ummar Musulmi jajen wannan babban rashi da kuma addu’ar Allah Ya sa Aljanna ce makoma a gare shi.
Marigayi Sheik Abubakar Giro Argungu an shirya za a masa sallar jana’iza ne da misalin karfe 2 na rana a Jihar Kebbi.