An shiga rudani bayan fitaccen jagoran Darikar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya nesanta kansa da wani sauti da ke yawo cewa ya bukaci magoya bayansa da su zabi dan takara shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.
A cikin wani sakon bidiyo da ya ci karo da wani sauti da a farko ya karade kafofin sada zumunta cewa yana goyon bayan Atiku, Sheikh Dahiru Bauchi ya bukaci jama’a su zabi duk wanda suke so a cikin ’yan takarar shugaban kasa.
- An kwato makamai fiye da dubu 10 sa’o’i kafin zabe
- NAJERIYA A YAU: Yadda Bangar Siyasa Ka Iya Dagula Lissafi A Wannan Zabe
- Duk da umarnin ’yan sanda, dubban magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kano
Ya bayyana cewa idan mutane sun tashi yin zabe, “Kowa ya fito lafiya, ya yi zabe lafiya, ya koma lafiya, ya yi zabe, ba mu nuna masa wanda zai zaba ba, ya zabi abin da yake so a ra’ayinsa a cikin mutanen da za a zaba.”
A farkon bidiyon Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana cewa, “Mutane da yawa sun tambaye mu, mene ne ra’yinku, na ce ba ni da ra’ayi a cikin siyasa.”
“Sun tambaya ko ina goyon bayan [wata jam’iyya (APC, PDP, NNNP, LP da sauransu)], to duk ba ni da ra’ayin mutum ko daya, amma dukkansu gaba daya ina goyon bayansu.
“kuma ba zai yiwu su ci gaba daya ba, daya ne zai ci, to Allah Ya zaba mana daya (mafi) alheri a ciki, Allah Ya zaba mana alheri, Allah Ya gyara mana kasarmu.”
“Allah Ya zaba mana alheri, Allah Ya gyara mana kasarmu, Allah Ya kiyaye kasarmu daga rikici da zalunci, Ya ba mu lafiya da zaman lafia da kwanciyar hankali.”
Sautin goyon bayan Atiku
Idan za a iya tunawa, a sautin da aka yada, wanda aka danganta da malamin, an ji yana cewa, “Na ji wasu mutane na cewa a zabi wanda zai dora a kan inda aka tsaya. To ai inda muka tsayan ba dadi muka ji ba, balle mu dora a kai. Mutum sai ya ji dadi yake cewa a kara min.
“Saboda haka ina kira da zabi inda za a sami sauki, ko Allah zai canza mana.
“Mutanena sun ba da shawara Atiku za su zaba, ni kuma tun da ga inda suka dosa ba zan rabu da su ba. Zan tsaya tare da su mu ga abin da Allah zai yi. Allah ya zaba mana abin da zai zama alheri,” in ji malamin.
Jajibirin zaben 2023
Wannan sa-toka-sa-katsi na zuwa ne a jajibirin zaben shugaban kasa da za a fafata tsakanin jam’iyyu 18, wadanda daga cikinsu ake hasashen daya daga cikin ’yan takarar manyan jam’iyyun APC, LP, NNPP ko PDP ne zai lashe.
A ranar Alhamis ne wannan dambarwa ta kunno kai, sa’o’i kadan kafin rufe yakin neman zaben da zai gudana a ranar Asabar 25, ga watan Fabrairu da muke ciki.
Za a gudanar da zaben ne tare da na ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa.