An tsaurara makatan tsaro a garin Kaduna a yayin da ake ci gaba da shari’ar jagoran mabiya akidar Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzky.
Aminiya ta shaida yadda aka fi tsaurara matakan tsaro a hanyoyi da sauran wararen da ke kusa da Babbar Kotun Jihar Kaduna a Titin Ibrahim Taiwo, inda ake shari’ar ta El-Zakzaky da matarsa Zeenat domin hana barkewar rikici.
Jami’an Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya sun kawo El-Zakzaky da matarsa kotun cikin tsauraran matakan tsaro domin halartar zaman kotun.
A zaman kotun na ranar Laraba ake sa ran alkalinta, Mai Shari’a Gideon Kurada, zai yanke hukunci kan bukatar El-Zakzaky na yin watsi da karar.
Gwamnatin Jihar Kaduna tana zargin El-Zakzaky da matarsa Zeenat kan kisa da tayar da zaune-tsaye da kuma gudanar da haramtaccen gangami da sauran laifuka.
Tun a 2015 aka tsare su bayan wani dauki-ba-dadi a mabiyan El-Zakzaky suka yi da sojoji a Zariya, wanda bayansa aka cafke mutane da dama daga cikin mabiyan malamin.
An kuma kai samame a Hussainiyyar mabiya akidar Shi’a da ke Zariya, wadda daga baya aka rusa ta gaba daya.
A zama kotun na ranar 1 ga watan Yuli, 2021, lauyan Zakzaky, Femi Falana SAN, ya bukaci ta yi watsi da karar, ta kuma ba da umarnin a saki malamin, tunda a cewarsa an kasa tabbatar da laifin da ake zargin sa a kai.
A nasa bangaren, lauyan Gwamnatin Jihar Kaduna, Dari Bayero ya gabatar da shaidu 15 domin tabbatar da zargin, daga cikin har da hafsoshi soji biyu da wani tsohon Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da likits da kuma jami’in dan sanda.