✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda su Kwankwaso suka yi Al-Kunut kan shirin ƙwace zaɓen Abba

NNPP ta shirya taron addu'o'in ne a Filin Mahaha, saboda zargin yunkurin saye alkalan kotun karrarkin zaben gwamnan ta bayan fage.

Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya harci taron addu’o’i na musamman da Gwamnatin Kano ta shirya kan zargin neman murde sakamakon zaɓen gwamnan jihar da jam’iyyarsa ta NNPP ta lashe a kotun sauraron kararrakin zaɓe.

Gwamnatin ta shirya taron addu’o’in ne a Filin Mahaha, saboda zargin yunƙurin saye alkalan kotun su yanke hukuncin da zai soke nasarar NNPP a zaben gwamnan ta bayan fage.

Kwankwaso tare Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Aminu Abdussalam na daga cikin ƙusoshin jam’iyyan NNPP da jami’an gwamnati da suka halarci taron addu’ar, wanda Babban Limamin Juma’a na Ƙofar Nassarawa, Dokta Ashir ya jagoranta.

Limanin ya roƙi Allah Ya wargaza masu shirya wa shugabannin jihar zagon ƙasa.

“Ya Allah, ga shugabanninmu nan da Ka albarkace mu da su, muka zaɓe su don ƙashin kanmu. Muna rokon Ka Ya Allah, Ka kare mana su, Ka shiyatar da su.

“Ya Allah, maƙiyan al’ummar jihar nan suna ƙulla wa shugabanninmu zagon ƙasa, don haka muna roƙon Ka Ya Allah, Ka wargaza makirci maƙiyanmu, Ka wargaza maƙiyan Jihar Kano a duk inda suke.

“Ya Allah maƙiyan jiharmu suna neman a murde abin da muka zaba ta bayan fage. Ya Allah, Ka wargaza su, Ka rikita su,” kamar yadda limamin ya yi addu’a.

Ya ci gaba da cewa, ”Ya Allah Ka tabbatar da aminci a Jihar Kano, Ka albarkaci kasuwanninmu da makarantunmu da gonakinmu da kuma kasuwancinmu .

“Ya Allah Allah Ka yi wa shugabanninmu albarka, ka rusa maƙiyansu.”

APC na ƙalubalantar nasarar Abba a Kotu

Jam’iyyar APC tana ƙalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf a zaɓen gwamna a gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Jihar Kano.

A ranar Litinin kotun ta kammala karɓar bayanan ƙarshe na ɓangarorin da ke shari’ar, inda ta ce nan gaba za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci.

Zargin murɗe zaben Abba

Gabanin haka an yi ta zargin cewa wasu lauyoyi na yunƙurin ba wa alƙalan kotun, lamarin da ya sa ɓangarorin NNPP da APC a jihar suke zargin juna kan batun.

Daga baya gamayyar kungiyoyin fararen hula masu sa ido na Jam’iyyar NNPP kan zaɓe, sun yi tattaki zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Kano inda suka buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu ya baki cikin lamarin.