✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sharhin littafin ‘My Literary Journey’ Rayuwa da ayyukan adabi na Dokta Bukar Usman

Dokta Bukar Usman tsohon Babban Sakatare ne a ofishin Shugaban kasa da ya zabi kasancewa marubuci a tsawon shekaru, bayan ya yi ritaya daga aikin…

Dokta Bukar Usman tsohon Babban Sakatare ne a ofishin Shugaban kasa da ya zabi kasancewa marubuci a tsawon shekaru, bayan ya yi ritaya daga aikin gwamnati. Hasali ma, saboda dimbin ayyukan da suke jibge a ofishinsa, wannan aiki na rubuce-rubuce bai samu ranar shanya ba sai bayan ya ajiye aiki, duk kuwa da cewa hikima da basirar rubuce-rubucen na nan tare da shi. A lokacin da yana dan yaro karami, ya fa’idantu da Makumtha, wato yanayin sauraren tatsuniya da dare cikin harshensa na Bura a garin Biu da ke Jihar Bornon Najeriya. Wannan lokaci shi ne damarsa ta farko cikin sauraren tatsuniya, amma kuma da yake aiki na gaba, abubuwa da yawa sun gudana a wannan fanni, musamman ma da yake Bukar ya tattara hikimarsa ta rubutu ya mika ta ga adabi.
Tarihin gwagwarmayar Dokta Bukar a matsayinsa na marubuci na kunshe ne a wani sabon littafinsa mai suna ‘My Literary Journey’ (Rayuwar Dokta Bukar Usman Da Ayyukansa Na Adabi), wanda kamfanin wallafa na Klamidas ya buga a shekara ta 2013. Gwagwarmayar tasa ta fara ne a 1992, lokacin da ya fara da rubuta tarihinsa cikin wani littafi da ya sanya wa suna  ‘Hatching Hopes.’ A ciki, ya fara ne da bayanin irin kwarewarsa da ta abokanan aikinsa da kuma ta wadanda ke karkashinsa, musamman bayan sun tashi daga aiki. Daga nan kuma sai kallo ya koma sama, wato mutane suka fara sha’awar salon rubutunsa kuma suna bayyanawa cikin sharhi a rubuce. Daga cikin irin wadannan mutane akwai Lamine Ojigbo, marubucin littafin ‘200 Days In Eternity (1979)’ yana cewa: “Ayyukan Bukar suna da dadin karantawa amma kuma akwai bukatar a kara ingancin labaran ta yadda za su yi armashi.”
A ranar 14 ga Agustan 1992, sai Madam Jane Emokpae, wata mai aikin akawu a ofishin Bukar da ke Legas ta rubuto cewa: “Tarihin rayuwarka yana da muhimmanci kuma ya kayatar da ni. Bugu da kari, yana kunshe da barkwanci da ya sa ya yi dadin karantawa.” Da samuwar irin wadannan sharhi na karfafa gwiwa, sai himma da kwazo suka karo cikin rubuce-rubucensa na adabi. Sai dai kuma mafarkinsa bai tabbata ba sai a 1992, lokacin da ya yi ritaya. Daga nan kuma sai cikakkiyar damar da ake nema ta samu ta ci gaba da rubuce-rubuce, da yake a yanzu babu ayyukan ofis. Nan da nan sai basira da kuma aiki da basira suka ci gaba da bayyana gadan-gadan, musamman ma da fitowar littafinsa na farko mai suna ‘The Beautiful Bride And Other Stories’ a 2005. Bayan wannan kuma sai littafin ‘Hatching Hopes’ da aka buga a 2006, wato shekaru 14 bayan kalailece shi.
Daga 2005, Bukar ya wallafa littattafai fiye da 20 kan adabi, ciki har da littafinsa na ‘Taskar Tatsuniyoyi’ mai shafi 652. A gaskiya ma, littattafai 26 ya wallafa, daga cikinsu 15 ne a cikin Hausa kamar haka: ‘Marainiya Da Wasu Labarai,’ ‘Jarumin Sarki,’ ‘Yarima Da Labi,’ ‘Tsurundi,’ ‘Sandar Arziki,’ dankutungayya,’ ‘Gwaidaraya,’ dan Agwal’ da ‘Tsohuwa Da ’Yanmata Uku.’ Sauran su ne: ‘dankuchaka,’ ‘Al’ajabi,’ ‘Yargata,’ ‘Duguli dan Bajinta,’ ‘Muguwar Kishiya’ da kuma ‘Taskar Tatsuniyoyi’ (Littafi 1- 14). Littattafansa wadanda ba na zube ko adabi ba sun hada da na zamantakewa da siyasa: ‘Press, Policy and Responsibility,’ ‘The Interface of the Muse and Gobernment Protocol,’ ‘Democracy, Human Right and National Stability’ da kuma ‘boice in a Choir: Issues in Democratisation and Stability in Nigeria.’ Cikin shekaru 20, marubucin ya gabatar da ayyuka daban-daban wadanda kuma bayanansu na cikin wannan sabon littafi na rayuwa da ayyukansa na adabi. Sai dai kuma wannan littafi ya tanadi abubuwa da yawa cikin salo da kwarewa.
Da farko dai marubucin ya fara ne da tsokaci kan ayyukan magabata, sannan sai ya daidaita matsayinsa cikin rubutunsa. Ta wannan salo, ya waiwaiyi marubuta na gida da kuma na waje da kuma masu sukar ayyukan da aka yi duk cikin ci gaba da bunkasar hikima. Daga cikin ’yan Najeriya akwai Abubakar Gimba da Wale Okediran da kuma Ogaga Howodo. A irin nasa salon rubutun, Bukar ya bayyana cewa: “Ni ina rubutu ne tamkar ina magana ko kuma na yi niyyar yi.” Ya yi amanna da wannan salo ne a sanadiyyar tasirin aikin Gerald Lebin mai suna ‘A Brief Handbook of Rhetorics’ wanda a ciki ya yi bayanin cewa: “Domin dacewa da kowace irin manufa, salon bayani a rubutu shi ne jagora.”
Haka kuma ya amince da aikin Fowler mai suna ‘The King’s English’ wanda a ciki aka ayyana kyakkyawan rubutu a matsayin mai sauki, takaitacce kuma kai tsaye. Mawallafin ya kuma ba da goyon baya ga aikin Edwin Muir a matsayin jagora ga marubuci cikin dangantakarsa da mai karatu. Wato yanayin hawa da sauka na murya da kuma rashin soki-burutsu suna inganta sadarwa. Wannan shi ne matsayinsa kuma shi ne ma fi karbuwa a duniya gaba daya. A matsayinsa na marubuci, ya kuma yi godiya da jaddada muhimmancin ayyukan masu bita da editoci da kuma mawallafa. A nan ya yi jinjina ga Abidina Coomassie da Isma’ila Gwarzo da kuma mai wallafa ayyukansa wato Dube Nakolisa.
Gaskiyar maganar ita ce, Dube wanda marubucin waka ne da littattafan zube da yawa, shi ne ya ja hankalin Bukar ga nazarin tatsuniya kuma aka yi dace fannin ya zamo mai yalwa da albarka. A tsawon shekaru ashirin da ya yi yana rubuce-rubuce kan tatsuniya, an samu ci gaba a fagen adabi da zube. Ga misali, cikin shekaru biyu ya tattara tatsuniyoyi fiye da guda dubu daga al’ummar Biu. Wannan aiki na tattara da kuma adana tatsuniyoyi ya samu gudunmowa da kuma sa hannun mutane daban-daban kamar su Farfesa dandatti Abdulkadir da Farfesa Abdulkadir dangambo da Salisu Saleh Na’inna dambatta da Sa’idu Ahmed babura da sauransu.
Da yake shi ba Bahaushe ba ne amma kuma yana jin Hausa kamar jakin Kano, to wannan ta sa ya yi hadin gwiwa da wadannan masana kuma sakamakon da ake samu ya bayyana samuwar nasara. A yanzu ma dai, littattafansa sun samu karbuwa a sassa daban-daban na duniya. Haka kuma an amince da a yi amfani da su wajen koyarwa a makarantu. Ga misali, wata kungiya mai zaman kanta, IRENE Sahel da ke kasar Jamus ta nemi amincewar marubucin domin buga labarun cikin Hausar Boko da kuma Ajami, domin ilimantar da ’ya’ya mata a makarantun allo na kasar Nijar. A Kano, makarantar firamare ta Capital tana amfani da wasu littattafan a cikin manhajar karatu. Wannan aiki na Bukar yana nuna muhimmancin tatsuniya a ayyukan adabi da bunkasa al’umma da kuma mu’amala tsakanin al’ummu daban-daban.
Ta wannan haujin ne ma marubucin yake gudanar da bincike cikin tarihi da maganganun hikima a sassa daban-daban na duniya, domin fahimtar matsayin tatsuniya a adabin duniya. Wannan gagarumin nazari ya hada da al’ummar kasar Masar da Greece da Hindu da Iraniyawa da kuma Larabawa. Nazarin ya kuma hada da tatsuniyoyin Turawa da Amurkawa da kuma Sirilankawa. A nazarin kwatancen da ya gudanar, marubucin ya waiwayi aikin Fran Boaz wajen fahimtar yadda aka rika wadari da tatsuniyoyi daga wasu sassa na nahiyar Afirika zuwa wasu. Wannan bayani yana cikin gabatarwar da wani baturen Amurka Albert Helser ya yi a aikin Bukar Usman na tatsuniyoyin al’ummar Babur/Bura. Babu tababa a cikin ikirarin Boaz kan wannan batu, domin ya bayyana a sassa daban-daban, sai dai kuma akwai bukatar yin taka-tsan-tsan domin kauce wa cusa rudani cikin bayanan al’adun al’umma daga nazarce-nazarcen kwatance. Duk da cewa yawan kaura da aro da kuma tasirin al’adu su ne dalilan samuwar al’ummu a sassa daban-daban, to akwai kuma bambanci cikin hikimar wadannan al’ummun. Ga misali, Ulli Beier ya jaddada cewa: “Ana iya samun dacewar hikima tsakanin mutane a lokuta da kuma wurare mabambanta.”
Ya ba da misali da ginin dala da al’ummar Aztek na kasar Medico suka yi, duk kuwa da cewa ba su da wata dangantaka da Misirawa. Saboda haka, bai kamata nazarce-nazarcen kwatance su zama a sake ba, ta yadda za su hana tantance na asali ko nakwarai a irin aikin da Bukar yake yi na adabin al’ummar Biu. Babban abin da wannan littafi na ‘My Literary Journey’ ya kunsa shi ne hikimar adanawa. Littafin ba wai kawai bayanin hikimar marubucin ba ce da kuma kwarin gwiwa da ya samu, wato kuma wata dama ce ga mai karatu ta sanin wasu ayyukansa da aka riga aka wallafa da kuma irin martanin da ayyukan suka samu daga masana da manazarta a Najeriya.
A babi na uku na wannan littafi, an buga tarihin rayuwarsa a lokacin da yake yaro a garin Biu, da ya yi wa lakabi da ‘Garinmu.’ Rayuwarsa a Legas cikin shekarun 1960, ita ce ya kira ‘Rayuwar Legas.’ Dukkan wadannan ya zabo su ne daga littafin mai suna ‘Hatching Hopes.’ Daga wannan kuma sai batun Obama cikin mafarkin Martin Luther King Jnr, wato mafarkin da ya zamo gaskiya a sandiyyar kasancewar dan Afirika na farko da ya dare kujerar shugabancin Amurka. Wannan batu da kuma wasu kamar matsayin aikin dan sanda a Najeriya, suna rukuni na musamman. Ayyukan hikima da suka bayyana a wannan rukuni sun hada da: ‘War of the Witchdoctors’ da ‘The Forbidden Fruit’ da kuma ‘A Tale of Two Betrayals.’ Wadannan duka sharar fage ne, domin ainahin aikin na cikin littattafan da ke hannun mutane suna karantawa a halin yanzu. Galibi, irin wadannan kananan labarai kagaggu ne amma kuma suna kunshe da darussa na rayuwa. Sauran maganar ita ce, wannan littafi na ayyukan adabi bai kare da batun abin da marubucin yake yi ko tunanin yi ba. A maimakon haka, sai aka gabatar da bayanai na sharhi da martani daban-daban. A gaskiya ma yawan su ya mamaye fiye da rabin shafuka 228 na littafin gaba dayansa. Sai dai kuma saboda karancin fili, ba za a iya kawo dukkan wadanda aka buga ba daga bita ko sharhi ko matani ba.
Ga misali, akwai Ray Ekpu da Hussaini Tukur da Farfesa Kyari Tijjani da tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya da Gidado Idris, duk sun yi sharhi kan littafin ‘boice in a Choir.’ A gudunmowar Sakataren Gwamnati, cewa ya yi: “Bukar Usman ya yi amfani da salo mai armashi da kuma kwarewa wajen nazarin tsaro cikin yanayin tsarin dimokuradiyya a kasar nan.” Dangane da littafin ‘Hatching Hopes’  kuwa, mutanen da suka yi sharhi sun hada da Alhaji Abubakar Gimba da Janar Aliyu Muhammad Gusau da Farfesa Muhammad Nur Alkali da Farfesa Osato Giwa-Osagie da kuma Jakada (Dr.) George Obiozor. Abubakar Gimba cewa ya yi: “A gaskiya rubutun yana da kyau kuma ya kayatar da ni fiye da littafin ‘boice in a Choir.’  Kana da salo da zai kai ka ga kwarewa kuma kana da hikima.”
Akwai irin wadannan sharhi daga bakunan masana da yawa kuma an tanade su a karshen littafin a matsayin rataye. A gaba daya, sakonnin da ke cikin littafin ‘My Literary Journey’ ba su tsaya ga hanyoyin magance matsaloli ba, har ma da abin da T. S. Eliot ya ambata da gudunmowar gwanin rubutu cikin salon tafiya da lokaci.” A wannan littafi, Bukar ya tanadi dimbin ilimi a fannoni mabambanta da suka hada da al’ada da hikima da zamantakewa, musamman a cikin rayuwar al’ummun Najeriya a jiya da yau da kuma gobe. Littafi ne mai girma kuma kunshiyarsa tana da fadi, saboda haka salonsa ya kasance mai armashi.
Farfesa Yakasai malami ne a Jami’ar Usman danfodiyo Sakkwato, (+234) 08035073537 [email protected]