✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sharhin littafin Mene Ne Matsayarmu A Kan Jagorancin Izala?

Daga Abubakar Haruna Sunan littafi:         Mene Ne Matsayarmu A Kan                   Jagorancin Izala?Marubuci:           Muhammad Mu’azu A. JosWanda ya buga:   Umar…

Bangon Littafin Menene matsayarmu a kan jagorancin Izala.Daga Abubakar Haruna

Sunan littafi:         Mene Ne Matsayarmu A Kan                   Jagorancin Izala?
Marubuci:           Muhammad Mu’azu A. Jos
Wanda ya buga:   Umar Master ’Yan Taya Jos
Yawan Shafuka:   24

Hakika duk wanda ya karanta littafin da Muhammad Mu’azu Adam Jos ya rubuta mai suna ‘Mene Ne Matsayarmu A Kan Jagorancin Izala’ zai jinjina masa, ba don komai ba sai don kokarin da ya yi na ilimantar da jama’a kan wasu abubuwa da suke shige wa mutane duhu kan jagorancin kungiyar Izalatul Bid’a Wa Ikamatus Sunnah.
Marubucin littafin ya tattauna abubuwa kamar haka: Su wa suke wa’azi, kuma su wa ke taron karbar sadaka da gumba? Tatattun tambayoyi da gamsassun amsoshi, Wace majalisa ce a sama a kungiyar Izala? Takaitaccen tarihin Shaikh Yusuf Sambo Rigacukum da kuma Shugabanci a kungiyar addini. Muna fata Allah Ya hada mu a cikin ladar littafin.
Duk da cewa marubucin ya yi kokarin tsara littafin gwargwadon fahimtarsa amma duk da haka bai tsara littafin kamar yadda ya dace ba saboda bai bi ka’idojin zubi da tsarin littafi ba kamar yadda dokar buga littafi ta tanada.  Misali, bayan ya kammala gabatarwa da dalilin da ya sa ya rubuta littafin, a maimakon ya bayyana jerin abubuwan da ke cikin littafin da kuma shafukan da ya sanya su, sai ya fara da tarihin kungiyar Izala kai tsaye. Da kamata ya yi kamfanin da ya buga masa littafin ya ba shi shawara kan yadda ake tsara littafi. Ya kamata a ce marubucin ya tsara littafin yadda zai ja hankalin jama’a ta hanyar sanya hotuna masu jan hankali sannan bai kamata ya sanya hotonsa ba tare da hoton Shaik Yusuf Sambo ba. Kamata ya yi marubucin ya sanya hotonsa ko dai a bangon farko na littafin ko kuma daya daga cikin shafukan littafin. Ko da yake bai zama dole sai marubuci ya bayyana tarihinsa ba amma da yin haka zai kara wa littafin nasa kwarjini.
Ni a ganina kamata ya yi marubucin ya sanya wa littafin suna ‘Matsayarmu A kan Jagorancin Izala’ a maimakon ya sanya masa suna da sigar tambaya kamar haka: Mane ne Matsayarmu A Kan Jagorancin Izala? Yin haka zai rikitar da mai karatu ya hana shi gane jigon littafin tun da marubucin so yake jama’a su san matsayin bangaren Izala reshen Jos a kan jagorancin kungiyar Izala.
Babu shakka marubucin bai bi ka’idojin rubutun harshen Hausa ba, inda ya rika hada kalmomi da raba su ta yadda ya ga dama ba tare da lura da yadda ka’ida ta tsara ba. Tun daga sunan littafin da ke bangon littafin, marubucin ya yi kuskuren raba Kalmar: ‘Matasayar mu’ a maimakon ‘Matsayarmu.’ Ya hade Kalmar: ‘Akan’ a maimakon ‘A kan.’ Haka ma a shafi na uku ya hade Kalmar: ‘za’ace’ a maimakon ‘za a ce’ da Kalmar: ‘shine’ a maimakon ‘shi ne’ da kalmar: ‘dasu’ a maimakon ‘da su.’ Sannan ya rika rubuta kalmar: ‘wayan da’ a maimakon ‘wadanda’ da kalmar: ‘dani’ a maimakon ‘da ni.’
Marubucin ya rika rubuta sunayen mutane da kananan baki. Misali, a shafi na shida ya rubuta sunan ‘Alhaji lawal sambo’ a maimakon ‘Alhaji Lawal Sambo.’ A shafi na biyar ya rubuta sunan ‘sheikh Ahmad lemu’ a maimakon ‘Shaik Ahmad Lemu.’
Shafi na 24 ya yi kuskuren hade kalmar: ‘yasa’ da kalmar: ‘sukayi’ a maimakon ‘ya sa’ da ‘suka yi.’ Ya kamata marubucin littafin ya kiyaye cewa kalmomin ‘suke’ da ‘take’ da ‘muke’ da ‘kuke’ da ‘nake’ duk hade su ake yi. Haka ma kalmomin ‘takan’ da ‘mukan’ da ‘kukan’ da ‘yakan’ da ‘sukan’ da ‘kukan’ su ma hade su ake yi. Sannan tun daga farkon littafin har zuwa karshe ba a yi amfani da manhajar da ke sanya wa harrufa lankwasa ba kamar harafin ‘b’ da ‘d’ da ‘k.’ Wannan manhaja tana da amfani domin idan babu ita rubutun Hausa ba zai karantu yadda ake so ba.  
Kodayake marubucin littafin ya yi kokarin takaita littafin amma da kamata ya yi a ce ya fadada shi ta yadda zai yi bayanin abubuwa dalla-dalla don mai karatu ya samu amsar tambayoyin da ke zuciyarsa. Misali, ya kamata da ya kawo cikakken tarihin kungiyar Izala da cikakken tarihin Shaik Yusuf Sambo da tarihin Shaik Isma’ila Idris da tarihin Shaik Muhammad Sani Yahya Jingir. Sannan da hotunan malaman da za su zama hujja ga mai karatu ko mai kalubalantar gaskiyar abin da da aka yi rubutun a kansa.
 Ina fata marubucin zai sake fadada littafin ta hanyar bin ka’idojin rubutu da salo mai kyau da zubi da tsari mai kayatarwa ta yadda jigon littafin zai fito fili ba tare da mai karatu ya sha wahala ba, domin yin haka shi zai fito da manufar littafin sakon da marubucin yake so ya isar ya samu isa ga jama’a ba tare da wata mushkila ba.

Abubakar (08027406827) ya rubuto sharhin nan daga Legas