✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster) (1)

A yau za mu zan dakata da bayani kan maudu’in da muka dauko makonni uku da suka gabata don yin bitar littafi na farko da…

A yau za mu zan dakata da bayani kan maudu’in da muka dauko makonni uku da suka gabata don yin bitar littafi na farko da aka wallafa kan fannin kwamfuta.  Da zarar mun gama wannan bita in Allah Ya so, za mu ci gaba da bayanin da muka dauko a baya.  Da fatan za a fa’idantu da wannan dan takaitaccen sharhi.  A ci gaba da kasancewa tare da mu.

A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019 ne aka kaddamar da littafin Malam Salisu Hassan wanda aka fi sani da “Webmaster” a garin Kaduna. Malam Salisu Hassan dai Malami ne mai karantar da ilimin kwamfuta a shahararriyar makarantarsa da ke unguwar Sanusi mai suna: “Duniyar Computer”, kuma mawallafin mujallar “Duniyar Computer” dai har wa yau.  Wannan littafi nashi, duk da cewa akwai wasu littattafai da aka rubuta a baya kan kwamfuta cikin harshen Hausa, sai dai, a hukumance, ba a samu irin wannan ba. Hakan ya faru ne saboda dalilai da dama.  Na farko dai shi ne littafi mafi girma da aka taba wallafawa a wannan fanni.  Shi ne littafi mai dauke da lambar jerin littattafan da aka rubuta a kasar nan, wato: ISBN.  Kuma littafi ne da ya kandamo abubuwa masu muhimmanci kan ilimin kwamfuta da hakikanin abubuwan da ta kunsa.

Littafin, wanda aka yi wa suna da: “Kwamfuta – Ilimin da Kowa Ke Bukata”, mai shafuka 353, yana dauke ne da babuka 11, a karshensa kuma aka bibiyi babukan da jerin kalmomin kwamfuta guda 500 tare da ma’anoninsu. Ina daga cikin wadanda suka yi bitar wannan littafi makonni uku kafin kaddamar da shi.  Don haka na ga dacewar rairayo muhimman abubuwan da littafin ya kunsa, don fa’idar masu karatun wannan shafi.  Hakika kaddamar da wannan littafi ba karamin ci gaba bane ga al’ummar Hausa a wannan zamani.  Ko ba komai dai, zai kara fadada fahimtar al’ummar Hausawan wannan zamani kan fasahar sadarwa na zamani; domin kwamfuta ita ce asalin dukkan wani ci gaba da ake samu a wannan fanni a duniya yanzu.

Malam Salisu ya kasa littafin ne zuwa bangare uku, duk da cewa bai bayyana hakan ba a zahiri ko a rubuce.  Bangaren farko ya kunshi Mukaddima ne. Wannan shi ne babi na daya, kuma mawallafin littafin bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayanin ma’anar kwamfuta, da nau’ukan bayanan da take mu’amala da su, irin su “data” da “information”.  Wadannan su ne nau’ukan bayanan da kwamfuta ke mu’amala da su.  Ko dai ya zama bayanai ne da ake shigar mata, take sarrafawa don bayar da ma’ana; wannan shi ake kira “data”.  Sai kuma nau’ukan bayanai sarrafaffu, wadanda duk mai karatu zai iya gane me suke nufi kuma ya fitar da hukunci daga abin da suka kunsa.  Wadannan su ake kira “information”.  Daga nan ya yi bayani kan irin ayyukan da kwamfuta ke iya gudanarwa.  A karshen babin ya kawo tarihin kwamfuta a takaice.  A Babi na biyu kuma mawallafin ya yi bayani kan karkasuwan kwamfuta ne ta amfani da ma’aunai daban-daban – tun daga farkon kwamfutar da aka fara kerawa zuwa zamanin da muke ciki yanzu.

Bangare na biyu na daukene da babuka guda shida (babi na uku zuwa babi na takawas).  Wannan bangaren ne ya yi bayani filla-filla kan gangar-jikin kwamfuta, wato: “Hardware” Kenan.  A Babi na uku mawallafin ya yi bayani kan ma’anar kalmar “Hardware”, da bangarorinta irin su na’urorin shigar da bayanai, da na fitarwa, da na aiwatar da sadarwa, da ma’adana, da bangaren sauti da na wutar lantarki duka.  Bayan wannan gabatarwa kan gangar-jikin kwamfuta a Babi na uku, sai mawallafin ya bibiyi babi na hudu zuwa na takwas da bayani filla-filla kan wadancan bangarori da ya fara bayaninsu a babi na uku.  Misali, a Babi na hudu ya yi bayani kan bangarorin shigar da bayanai ne ga kwamfuta, wato: “Input Debices”. Wannan ya hada da allon shigar da bayanai (Keyboard), da beran kwamfuta (Mouse), da na’urar daukan hoton bayanai (Scanner), sai kuma na’urorin shigar da sauti ko murya.  A Babi na biyar kuma marubucin ya fayyace bayani kan bangarorin fitar da bayanai daga kwamfuta, wato: “Output Debices”. Na’urorin sun hada da talabijin kwamfuta (Monitor), da na’urar haskaka bayanai (Projector), da lasafika, da na’urar dab’i, da dukkan nau’ukan wadannan na’urori.

Bayani kan ma’adanar kwamfuta, wanda mawallafin ya kira da suna: “Ma’ajiya”, yana kunshe ne cikin Babi na shida, wanda ya yi wa lakabi da: “Storage Debices”.  Karkashin wannan Babi Malam Salisu ya fayyace ma’ana da nau’ukan ma’adanar kwamfuta, inda ya jero shahararru daga cikinsu, irin “Hard Disk Dribe – HDD”, da “Solid State Dribe – SSD”, da wasu ma’adana na musamman irin su: “Floppy Disk”, da “Optical Disc” – kamar su: CD da DBD da kuma Blue Ray Disc.  Marubucin ya bambance tsakanin ma’adanar da ake iya shigar mata da bayanai ta bangaren mai mu’amala da kwamfuta, da wacce ba a iya shigar mata; sai dai a wadatu da abin da ta zo da shi.