✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sharhin fim ɗin ‘Aisha Biyu’

Aishas Biyu fim ne da aka yi domin nuna yadda ake iya tasowa cikin rayuwa mai dadi.

Take: Aisha Biyu Darakta: Shareefah Abiola-Andu Shekara: 2023 Tsawon fim: Awa 1 da minti 26

Taurarin finafinan Aisha Biyu su ne fitattun jaruman Masana’antar Kannywood mata guda biyu, wato Rahama Sadau da Maryam Booth, inda suka fito suka taka rawa a matsayin kawayen juna da rikici ya barke a tsakaninsu.

An yi fim din wanda ya ƙunshi barkwanci da alakar dantangaka da siyasa gami da matsalolin burin rayuwa da yadda irin matsalolin yau da kullum suke iya bata zumunci da zamantakewa har a iya samun samu yi a 2023.

Kawayen wadanda suka taso a tare tun suna yara, wato A’isha da A’isha, inda bayan sun girma suka isa aure, sai su biyun suka auri wasu fitattun ‘yan siyasa.

Ana cikin haka ne sai sabani ya kaure a tsakaninsu a sanadiyar mazajensu saboda bambancin siyasa.

Dan siyasa Jamal Jibril (Paul Utomi) wanda yake da burin samun tikitin takarar Mataimakin Gwamna, amma saboda wasu matsalolin haraji da sauransu, sai aka kwace tikitin daga hannunsa aka ba wa Ibrahim Yusuf (Akeem Ogara).

Jamal ya yi zargin cewa, akwai hannun Ibrahim a matsalolin da suka sa aka kwace masa tikitin takarar, amma Ibrahim ya dage kai da fata shi bai da masaniya.

A daidai lokacin da suke tashin-tashina a kan siyasarsu, matansu biyu ne suke shiga tsaka-mai-wuya, kasancewar tsofaffin kawaye ne da suka taso tare, amma kuma mazansu na cikin wata rigima babba saboda siyasa.

Hakan ya sa wata kawarsu ta daban, Halimah (Shushu Abubakar), ta shiga tsakani, inda ta dage wajen kokarin kawo masalaha da sulhu a tsakanin kawayen domin a gano bakin zaren, tare da warware rikicin nasu, wanda suka fara a sanadiyar rikicin siyasar mazajensu.

Iyke Okechukwu ne ya jagoranta.

Aishas Biyu fim ne da aka yi domin nuna yadda ake iya tasowa cikin rayuwa mai dadi cikin dangantaka da zumunci da son juna, amma kwatsam abin duniya ya zo ya raba.

Aiki ne da aka zurfafa tunani wajen tsarawa da kuma kayayyakin aiki masu nagarta na zamani domin aikin ya fita fes.

Jaruman sun yi kokari wajen fitar da labarin kamar yadda aka tsara, sannan sakon ya fito fili.

Sai dai kamar yadda aka saba, komai kyawun fim, dole a samu wasu matsaloli ko tsaiko. Misali, tun a farkon fim din an gane cewa abokan guda uku, biyu za su iya samun matsala.

Kuma da rigimar ta kunno kai, a bayyane take cewa Halimah ce za ta warware matsalar tare da kawo maslaha.

Haka kuma, makirce-makircen da ake kullawa tsakanin kawayen ba su bayyana ba sosai ba a fim din, amma mai hangen nesa zi iya gano yadda aka rika kitsa makircin.

Don haka ya kamata a gane cewa, su kansu jarumai da masu shirya finafinan sukan samu tsaiko wajen fitar da sawu sakonnin.

A bangaren kananan jaruman kuwa, duk da cewa ba kwararru ba ne, sun yi kokari matuka wajen taka rawar da aka ba su. Sannan an nuna tasirin addini sosai a fim din.

A bangaren kayan aiki, daukar bidiyo da tacewa duk an yi kokari.

Bangaren sauti, ya fita fes. Sannan masu shirya fim din da darakta kowa ya yi iya bakin kokarinsa domin nishadantar da masu kallo.

Aminiya ta kalato ne daga www.whatketmeup. com