✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sharhi: Dangantakar tatsuniya da tarihi a adabin al’ummun duniya

Sunan Littafi: Folklore and History: The Twin Rikers of World HeritageSunan Marubuci: Bukar UsmanKamfanin Wallafa: Klamidas Communications Ltd. AbujaShekarar Wallafa: 2013Yawan Shafuka: 67Farashi: Ba a…

Sunan Littafi: Folklore and History: The Twin Rikers of World Heritage
Sunan Marubuci: Bukar Usman
Kamfanin Wallafa: Klamidas Communications Ltd. Abuja
Shekarar Wallafa: 2013
Yawan Shafuka: 67
Farashi: Ba a fada ba

Littafin ‘Folklore and History: The Twin Rikers of World Heritage’ yana kunshe ne da muhimman bayanai da suka danganci tatsuniya da almara da kuma yadda wadannan jigogi na adabi suka zama ruwan dare gama duniya, kasancewar a kowace nahiya akwai irin nata. Littafin ya samu ne a sakamakon ingantaccen binciken da marubucin ya gudanar dangane da al’amarin. Tun da farko, kunshiyar littafin ya samu ne a sakamakon laccar da marubucin ya gabatar a taron kasa-da-kasa dangane da adabin gargajiya, wanda aka gudanar a ranakun biyu zuwa biyar ga Afrilun da ya gabata a Jami’ar Bayero Kano.
Babban jigon littafin shi ne, bayyanawa da nuna tasiri da muhimmancin tatsuniya da almara ga al’umma da kuma yadda suka danganci tarihi. Ba nan abin ya tsaya ba, littafin kuma ya nuna yadda tatsuniya da tarihi suka kasance tamkar ruwan koguna biyu da ke malala cikin babban tafki guda. Cikakken nazarin da marubucin ya yi dangane da maudu’in littafin ya tabbatar da muhimmancin tatsuniya da almara wajen bunkasa ilimi da cusa tarbiyya da nishadantarwa ga musamman yara da kuma al’umma baki daya. Haka kuma, ya tabbbatar da cewa, tatsuniya da al’amara, hanyoyi ne na adana tarihi da al’adun al’umma.
A gabatarwar littafin, wadda ta fara daga shafi na 1 zuwa na 6, marubucin ya bayyana yadda ya sadaukar da lokacinsa wajen bincike game da tatsuniya da almara na al’ummarsa ta Babur/Bura da ke Jihar Borno kuma ya danganta su da na al’ummar kasar Hausa. Haka kuma, ya bayyana yadda ya tattara tatsuniyoyi masu yawa, wanda haka ya ba shi dammar rubuta ingantattun littattafan ‘Taskar Tatsuniyoyi’ guda 14, wadanda ya killace kuma a babban kundi guda daya, domin amfanin al’umma.
A babi na biyu kuwa, wanda ya faro daga shafi na 7 zuwa na 12, marubucin ya yi kokarin bayyana yadda tatsuniya da almara suka zama tamkar ruwan dare gama duniya, musamman ma yadda tatsuniyoyin suka yi kamanceceniya tsakanin na wannan nahiya zuwa na waccan. Ya nuna yadda cinikin bayi da ya gudana a shekarun baya ya zama tsanin yada tatsuniyoyi da almara da al’adun mutanen Afrika zuwa Amurka da sauran yankunan duniya. Ya kawo misalin yadda tatsuniyar ta zama hanyar adana tarihin al’umma. Labarin jarumai kamar Bayajidda a kasar Hausa da Oduduwa a kasar Yarabawa da Yamtarawala a kasar Biu, duk misalai ne na yadda tatsuniyar ta kasance hanyar taskance tarihi da al’ada.
A babi na uku kuwa, wato daga shafi na 13 zuwa na 24, marubucin ya yi nazari ne game da tatsuniya da almara na sassan duniya. Ya kawo misali da tatsuniyoyin da aka samu a kasar Masar da Indiya da Iran, kamar kuma yadda ya ce a kasar Turai ma an samu. Ya kara da cewa, wasu daga cikin labarun littattafan marubuci Shakespeare, sun samo asali ne daga tatsuniyoyi da almarar yankin nasu.
Daga babi na hudu, har zuwa na bakwai, wato daga shafi na 25 har zuwa na 51, bayanai sun gabata na bukatar marubucin ga marubuta, manazarta da malamai da su maida hankali wajen bincike game da tatsuniyoyi. Ya nuna cewa tamkar misalin mai hakar gwal ne, duk lokacin da ya haka da zurfi, zai kuwa samo albarka. Don haka akwai bukatar a ci gaba da bincike, domin tattara tatsuniyoyi da almara da ke kinshe cikin al’ummominmu, domin amfanin na gaba.
Babu shakka, ya dace a yaba da kokarin Dokta Bukar Usman, yadda ya jajirce yana hidima ga adabi. Haka kuma ya dace a tashi tsaye wajen amsar shawararsa, cewa masu bincike su ci gaba da bincike game da al’adu, tatsuniyoyi da almarar al’ummarmu, domin kuwa tsofaffin mutane suna mutuwa, suna tafiya da ilimin da ke kinshe a tare da su na al’ada da tarihi. Idan ba a yi haka ba, to babu shakka nan gaba al’ummarmu za ta rikide, ta mance da al’adunta, ta rungumi na wasu.