✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shanyar mahaukaci

A asibitin mahaukata ne, sai wani mahaukaci, mai suna dankawu ya tsunduma cikin wani katon tankin ruwa. Da wani mahaukacin, wai shi Sallau ya hango…

A asibitin mahaukata ne, sai wani mahaukaci, mai suna dankawu ya tsunduma cikin wani katon tankin ruwa. Da wani mahaukacin, wai shi Sallau ya hango shi yana neman mutuwa, sai nan take ya je ya tsamo shi. Jin wannan labari sai babban likitan asibitin ya zaci cewa lallai Sallau ya warke, kuma ya kamata a yi masa dubawar karshe a sallame shi. Likita ya kira shi yace: “Amma fa Sallau ka burge ni yadda ka tsamo dankawu daga tankin ruwa ka ceci ransa. Saboda hak…” Kafin ya karasa magana, sai ga wani a guje yana cewa: “Ai dankawu ya rataye kansa ya mutu.” Jin haka sai Sallau ya ce: “Kash! Wallahi ba kashe kansa ya yi ba. Ni ne na rataye shi don ya bushe, bayan na tsamo shi daga tankin ruwa!”
Daga Aminu dankaduna Amanawa 07065654787