✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shamsu da Maryam sun zama jakadan kamfanin Frufru

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Shamsu dan’iya da kuma jaruma Maryam Yahya sun zama jakadun kamfanin lemon Frufru. Jaruman sun sanya hannu a yarjejeniyar da suka…

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Shamsu dan’iya da kuma jaruma Maryam Yahya sun zama jakadun kamfanin lemon Frufru.

Jaruman sun sanya hannu a yarjejeniyar da suka cimma da kamfanin ne a Kano a ranar Lahadin da ta gabata.

A lokacin da Aminiya ta tattauna da jarumi Shamsu wanda ya fito a manyan fina-finai da suka hada da ‘Shakka’ da ‘Ga Mu Nan Dai’ da kuma ‘Rariya’ ya bayyana farin cikinsa dangane da wannan mataki da ya taka.

“Kamfanin kamar Frufru ya amince ka zama jakadansa ka san ba karamin abu ba ne, inda hakan ya tabbatar da ya yarda da halayenka da dabi’unka da mu’amalarka da kuma yadda kake da farin jini da samun karbuwa a wurin masu kallo.”

Ya bayyana za su yi aiki da kamfanin har tsawon shekara daya, inda zai kasance a sahun gaba wajen yi musu tallace-tallace a kafafen sadarwa da suka hada da Instagram da twitter da facebook, sannan za a sanya fuskokinsu a allunan tallace-tallace a birane da garuruwan kasar nan da dai sauran aikace-aikace.”

Ya bukaci masoyansa su ci gaba da yi masa addu’a, domin addu’ar masoyi ba ta faduwa kasa banza.

Ya kuma gode wa masoyansa sakamakon gudunmuwar da suke ba shi, inda hakan ne ya sanya ya taka matsayin da yake kai, kuma ba don su ba, to ba zai samu tsanin hawa matakin da yake kai a yanzu haka ba.

“Masoyana su ne abin alfaharina, ba don su ba, to ba zan kai ga matsayin da nake ba. Allah Ya saka musu da alheri.”