✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shahararren Mawaki Naira Marley ya gurfana a kotu

’Yan sanda a jihar Legas sun kama shahararren mawakin nan na kudancin Najeriya, Azeez Adeshina Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley bisa zargin…

’Yan sanda a jihar Legas sun kama shahararren mawakin nan na kudancin Najeriya, Azeez Adeshina Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley bisa zargin karya dokar hana zirga-zirga a tsakanin jihohi.

A ranar Alhamis ’yan sanda a Yaba, Legas, suka kama Naira Marley tare da manajansa Seyi Awonuga, suka kuma gurfanar da su a kotun tafi-da-gidanka da ke Oshodi.

A ranar 13 ga watan Yuni mawakin ya yi bulaguro daga Legas zuwa Abuja da zummar yin waka a can.

Tafiyar tasa ta tayar da kura saboda a lokacin ana tsaka da dokar hana taruka da kuma hana zirga-zirga a tsakanin jihohi.

Kakakin ’yan sandan Legas SP Bala Elkana ya ce mawakin ya saba dokar kiyaye cututtuka masu yaduwa ta jihar, wadda za a iya hukunta wanda ya sabata ta karkashin dokar lafiyar al’umma ta jihar.

Bala Elkana ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumarsu kuma kotun ta ci tararsu naira dubu 100 ko wanne.