✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sha’awar farauta ce ta sa na shiga sana’ar busa kaho -Bako Maikaho

Wani matashi mai busa kaho, mai suna Malam Isah Bako Maikaho, dan kimanin shekara 19 a duniya da ke zaune a kasuwar Mil 12 a…

Wani matashi mai busa kaho, mai suna Malam Isah Bako Maikaho, dan kimanin shekara 19 a duniya da ke zaune a kasuwar Mil 12 a Legas,  ya ce sha’awar farauta ce ta sa ya mayar da busa kaho sana’a.
Malam Isah Maikaho, dan asalin garin Bargoni da ke karamar Hukumar kiru a Jihar Kano, wanda ke zaune a kasuwar Mil 12, ya shaida wa Aminiya, a wata tattaunawa da suka yi, cewa ba gadon busa kaho ya yi ba.
“Gaskiya ba gado na yi ba, harkar farauta da nake yi, shi ya sa nake sha’awar busa kaho a kodayaushe kuma har ma na mayar da ita sana’a. Na fara hura kaho tun ina karami, kuma yau na yi shekaru kimanin 12 ina yin ta a masayin sana’a. Ina jin dadi kwarai da gaske idan ina busa kaho. Na tsunduma cikin wannan harka da kaina, tun ina koyo har na zama wanda ya kware a harkar busa kaho. Babu taken da ba zan iya busawa ba, kuma babu yadda ba zan iya hura shi ba. Idan ina so ya yi kara sosai, akwai yadda nake yi, idan kuma ina so kada ya yi kara sosai, akwai yadda nake yi”. Inji shi.
Malam Isah ya bayyana cewa ya mallaki gidaje da gonaki da kadarori da dama sakamakon busa kahon da yake yi wa jama’a.
Ya ce harkar busa kaho tana sanya wa mutum ya san mazaje da yawa da kuma fitattun mutane.
Ya bayyana cewa da kahon naman dajin nan da ake kira Mariri yake amfani wajen hura kahon, tare da sanya fata a jikinsa. “Wannan kahon Mariri ne, wanda ake yi masa kirari da Mariri mai kukan dadi. Shi na samu na gyara na nade shi da fata. Na yi masa aiki sosai domin na kashe kimanin Naira dubu hudu da dari biyar kafin kahon ya zama cikakken kahon da za a iya hurawa. Shi ya sa yake ba da sauti mai dadi. Shi kaho, idan kana so ya yi amo mai dadi, sai ka gyara shi, ka hora shi”. Inji shi.
Ya yi godiya ga Allah saboda rufin asirin da Ya yi masa sakamakon busa kaho, inda ya ce yakan yi wasa duk lokacin da wani biki ko taro ya taso a kasuwar Mil 12.