Manchester United ta yi ban kwana da Europa League, bayan da Sevilla ta sake maimaita tarihin fitar da ita daga gasar bana.
Sevilla ta yi nasarar cin kwallo 3-0 a wasa na biyu zagayen kwata-final da suka fafata a Sifaniya ranar Alhamis.
Kungiyar Sifaniya ta kai zagayen daf da karshe da jimillar cin 5-2 gida da waje, bayan da suka fara tashi 2-2 a Old Trafford ranar 13 ga watan Afirilu.
Minti takwas da fara wasa, Sevilla ta ci kwallo ta hannun Youseff En-Nesyri, sannan Lucas Ocampos ya zura ta biyu, amma aka soke cewar an yi satar gida.
Minti biyu da komawa zagaye na biyu ne Sevilla ta kara na biyu ta hannun Loic Bade, sai Youseff En-Nesyri ya zura ta uku a raga saura minti tara a tashi daga fafatawar.
Manchester United ta fitar da Barcelona da Real Betis a Europa League a kakar nan, bayan da ta fafata da Real Sociedad a cikin rukuni, Sevilla ta yi waje da ita.
Karo na biyu da United ta yi kuskuren da Sevilla ta zura mata kwallaye, ta kuma yi haka a fafatawa da Brentford a Agusta.
Karo na shida da kungiya daga Sifaniya ke fitar da Manchester United a gasar Zakarun Turai – uku daga ciki Sevilla ce ta cire kungiyar Old Trafford a 2017-18 da 2019-20 da kuma 2022-23.
Sevilla ce kan gaba a yawan lashe Europa League a tarihi mai shida jimilla, ita kuwa United guda daya take da shi.
United wadda ta lashe Carabao Cup a bana za ta buga daf da karshe da Brighton a Wembley a FA Cup, sanan tana ta uku a teburin Premier League.