✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar tankar mai: Sevilla FC ta jajanta wa al’ummar Jigawa

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Sevilla ta jajanta wa al'ummar Najeriya bisa rasuwar mutane sama da 150 samakon gobarar tankar mai a Jihar Jigawa

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Sevilla FC ta jajanta wa al’ummar Najeriya bisa rasuwar mutane sama da 157 samakon gobarar tankar man da ta fashe a Jihar Jigawa.

Sevilla ta bayyana jimaninta kan lamarin ne ta shafinta na sada zumunta tana mai jajanta wa ga duk wanda abin ya shafa.

Ƙungiyar wadda ’yan Najeriya biyu —Iheanacho da Ejuke — ke cikin tawagar ’yan wasanta

https://x.com/SevillaFC_ENG/status/1846982101222019360?t=T-G6sLf6R0mTXt6gLwzAwA&s=19

Galibin waɗanda ibtila’in na ranar Talata ta shafa matasa ne, masu cikinsu harda wani dan sandan kwantar da tarzoma mai muƙamin Sufeto.

Daga cikin mamatan har da wani ma’aikaci da ya kammala karatun difloma a fannin harhaɗa magunguna, Hassan Hamza tare da ’yan uwansa uku.

Aminiya ta ruwaito cewa wasu almajirai biyar ’yan makaranta guda suna daga cikin mamatan, da dai sauransu.

Hukumar ’yan sandan Najeriya ta ce mutane 94 ne suka mutu nan take bayan tashin wutar a lokacin da suka Kwalara man fetur da ke tsiyaya daga tankar man, bayan ta yi hatsari a garin Majia da ke Ƙaramar Hukumar Taura ta Jihar Jigawa.

Aƙalla mutane 125 ne aka binne gawarwakinsu a ranar Talata, inda akasarinsu suka ƙone ƙurmus.

Zuwa yammacin ranar Alhamis hukumomin Najeriya sun ce adadin mamatan ya ƙaru zuwa 157.

Waɗanda suka jikkata sakamakon ibtila’in na karɓar magani a asibiti a jihohin Kano da Yobe da kuma a jihar ta Jigawa.