✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Serena Williams za ta yi ritaya daga buga wasan tennis

Ta ce tana so ta ba iyalanta cikakken lokaci

Shahararriyar ’yar wasar kwallon Tenis din nan ta duniya, Serena Williams ta sanar da aniyarta ta yin ritaya daga yin wasan baki daya.

Ba’amurkiyar ’yar wasan ta sanar da aniyart tata ne bayan gasar wasan Tenis na kasa baki daya da aka kammala a kasar.

Serena ta ce za ta daina wasan ne domin ta ba wa mai gidanta, Alexis Ohanian, da kuma ’yarsu Olympia, cikakken lokaci tana mai cewa ritayar ta zama dole.

Bugu da kari, zakarar wasan na tenis ta ce tana ta son ta kara haihuwa kafin ta ciki shekara 40 cif w duniya.

“Ina mai shaida muke cewa ina da aniyar jan jiki daga wasan Tenis, zuwa ga wasu muhimman abubuwa da suke da muhimmanci a rayuwata,” inji Serena a hirarta da jaridar Vogue.

’Yar wasan ta kuma gode wa masoyanta, sannan ta ce za ta yi kewar wasan na tenis idan ta bar shi.