Kasar Senegal za ta sanya wa filin wasa sunan dan wasan gabanta Sadio Mane, don girmama shi biyo bayan lashe gasar cin kofin Afirka (AFCON) da suka yi.
Dan wasan mai shekara 29 a duniya, ya yi bugun karshe na fenareti a wasan karshe na gasar tsakaninsu da tawagar ’yan wasan Masar.
- Ban ji dadin sanya hotona a labarin rikicin Kannywood ba – Rahama Sadau
- ’Yan sanda sun cafke Abba Kyari sa’o’i bayan NDLEA ta ba da shelarsa
Dubban magoya bayan kasar ne suka yi dandazo a Dakar, babban birnin kasar na Senegal a ranar Litinin din da ta gabata don tarbar ’yan wasan.
Shi kuwa Shugaban Kasar, Macky Sall, bayan tarbar ’yan wasan ya musu 19 ta arziki, inda ya ba su kyautar kudi da gidaje.
An yanke shawarar karrama dan wasan ta sauya sunan filin wasa na ‘Sedhiou’ zuwa sunansa.
Gwamnatin kasar ta ce za ta karrama shi ne kan irin namijin kokarin da ya yi wajen jan ragamar tawagar sauran ’yan wasan kasar, har suka lashe kofin.
Filin wasan da ke Kudu maso Yammacin kasar, ana sa ran kammala gina shi a 2023.