Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo yana ganawar sirri da Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Prince Uche Secondus wanda rikicin jam’iyyar ya kazance.
Secondus ya isa gidan Obasanjo ke a Abeokuta a Jihar Ogun ne tare da wasu shugabannin jam’iyyar, a ranar Alhamis.
Nan take suka shiga ganawar sirri da Obasanjo wanda ya fice daga PDP a shekarar 2015; Duk da haka Obasanjo na da ta tasiri mai karfi a jam’iyyar wadda ya yi shugaban kasa a karkashin inuwarta sau biyu, daga 1999 zuwa 2017.
Ziyarar na zuwa ne lokacin da wasu shugabannin jam’iyyar suka tayar da kura cewa a a tsige Mista Secondus daga kujerarsa.
Suna zargin shugabancinsa da rashin iya kamun ludayin da ya sa wasu ’yan kwamitin amintattun jam’iyyar sauka daga mukaminsa wasu gwamnoni kuma suka fice daga jam’iyyar.
A makon jiya, wasu ’yan PDP sun yi zanga-zanga a Sakatariyar Jamiyyar ta Kasa da ke Abuja, suna neman Mista Secondus ya yi murabus.
Amma shugaban ya ce allambaram, daga bisani shugabannin jam’iyyar da ciki har daga gwamnoni da ’yan kwamitin amintattu suka sanya baki kurar ta lafa.
Bayan wani zaman da shugabannin jam’iyyar suka yi ranar Alhamis ne suka cimma matsaya a kan cewa a gudanar da baban taron jam’iyyar na kasa a watan Oktoba domin zaben sabbin shugabanni.
Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda Secondus dan jiharsa ne na daga cikin wadanda suka tsaya kai da fata wajen ganin an zabi sabon shugabanci.
Wike wanda a baya ya yi uwa ya yi makarbiya wajen ganin Secondus ya zama shugaban jam’iyyar ya babe da shi a kan rikicin shugabanci.