Fito da tsarin rabon aki ta wayar salula ya habaka kasuwancin taki a Jihar sakkwato, a cewar Shugaban kungiyar masu sayar da taki ta Jihar Sakkwato, Alhaji Malami.
Shugaban ya yi wannan kalamin ne a shagonsa da ke unguwar kara makon da ya gabata, lokacin da Aminiya ta ziyarce shi, domin sanin halin da kasuwancin takin zamani yake a jihar.
Ya ce gaskiya kafin shigowar wannan gwamnati ta Wamakko, muna cikin wahala, domin a yini da kyar za ka iya sayar da buhun taki 100 ga manoma, saboda tsadarsa, amma yanzu gwamnati ta shigo ciki sosai takan biya kashi 50 cikin 100 na kudin taki ga manoma, wanda yasa a yanzu taki ya yi sauki ga manomi, mukan sayar da fiye da 300 a yini, a cewarsa.
Shugaban masu sayar da takin zamanin a Jihar Sakkwato ya yaba wa gwamnatin jiha da tarayya kan mika masu wuka da nama kan harkokin kasuwancin taki, inda sauran jihohin kasar nan ba haka ba ne, ‘Gwamnatin Sakkwato ta hana mu barcin rana kasuwancinmu na takin zamani ya bunkasa sosai, don cibiyar da muke da ita a yanzu na sayar da taki sun fi a kirga sabanin inda aka fito da kasuwar ta mutu’ inji shugaba.
Ya ce kuskuren magana ne wani mutum cikinmu ko wani bangare daban ya ce gwamnati ba ta taimakam wa masu sayar da takin zamani ba, domin a can lokacin da ya wuce dillali yakan sayi taki a Jihar Legas buhu daya ya kama masa kusan 6000,amma a yanzu mutum yakan sayi buhun taki a Jihar Sakkwato kan kudi Naira 4000, wanda ya samu tallafin gwamnati yakan sayi takin kan kudi 2500, ka ga an samu sauki sosai daga gwamnati, wanda mu a wurinmu bunkasar kasuwarmu ne da harkar noma, ban da wannan tallafin na gwamnati da yawa akwai manoman da suka so jingine noma gaba daya saboda taki na gagararsu.
“Dukkan nau’in da muke da shi na takin zamani yanzu akwai shi sosai, kuma manoma sukan saye shi kan kari har da na ruwan da ya shigo, yanzu ya samu karbuwa. Rabon taki ta hanyar salula ya habaka kasuwancin takin zamani a jihar nan, saboda a yanzu manomi yakan yi rijista a gidansa kuma a dauki taki akai masa har bakin gidansa, ko a wane kauye yake, indai cikin jihar nan ne,” inji Shugaban.
Sayen taki ta waya ya habaka a Sakkwato
Fito da tsarin rabon aki ta wayar salula ya habaka kasuwancin taki a Jihar sakkwato, a cewar Shugaban kungiyar masu sayar da taki ta Jihar…