Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da Sufurin Man Fetur a Nijeriya, (NMDPRA), ta ce sayar wa ’yan bumburutun man a jarakuna ya saɓa doka.
NMDPRA ta bayyana hakan ne yayin da take barazanar ƙwace lasisin gidajen mai da ’yan kasuwar da aka samu da laifin ɓoye man fetur don sayar wa ’yan bumburutu.
Babban daraktan hukumar, Ogbugo Ukoha ne ya bayyana haka cikin wani bidiyo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, lokacin wata ziyarar ba-zata da wata tawagar hukumar ta kai wasu gidajen mai a Abuja babban birnin ƙasar.
A ’yan kwanakin baya-bayan nan ana fuskantar ƙarancin man fetur ɗin a wasu manyan birane da jihohin ƙasar.
A wasu jihohi, musamman da ke yankin arewacin ƙasar, ana fuskantar ƙarancin man, lamarin da ya tilasta wa wasu gidajen mai da dama rufewa, abinda kuma ya haifar da dogayen layuka a gidajen man da ke bayar da man.
Hukumar ta kuma ce sayar wa ’yan bumburutun man a jarakuna yana haifar da barazana ga kariyar muhalli.