Wasu bata-gari da ake kira ’yan Eriya Boys sun tayar da hargitsi saboda karancin sabbin takardun Naira da aka sauya da kuma wahalhalun da ’yan Najeriya ke fama da su a Jihar Legas.
A safiyar Juma’a ne dai ’yan Eriya Boys a unguwar Mile 12 da Ketu da Ojota suka kai farmaki kan matafiya tare da harbe-harbe.
- Ba za mu daina amfani da tsoffin kudi ba —El-Rufai ga Buhari
- Mai ciki ta rasu a asibiti a Kano saboda rashin sabbin kudi
An sami hargitsi a hanyar Legas zuwa Ikorodu da wasu sassan unguwar Agege, sai dai wakilinmu ya gano cewa zuwa yanzu kurar ta lafa.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da aukuwar tashin hankalin a yankin Mile 12.
Hundeyin ya ce “Gaskiya ne, mutanenmu suna can, an tura su wajen don karfafawa a zauna lafiya a can yayin da muke sa ido sosai da kuma kula da lamarin.”
Hundeyin ya sanar a haka ne a shafinsa na Twitter a martaninsa ga wani sako da ke neman karin bayani daga jami’in game da jita-jitar tarzomar.
A ’yan kwanakin nan an sami raguwar cunkoson ababan hawa matuka a kan titunan Legas, wanda aka danganta da matsalar sauyin kudi da kuma karanci ko tsadar man fetur.