Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni ya ce sauyi a jam’iyyar ya zama dole kuma babu makawa.
Da yake jawabi bayan taron kwamitin na farko bayan kafa shi, Buni ya ce rikicin shugabancin jam’iyyar ba bakon abu ba ne a manyan jam’iyyu, inda ra’ayoyi kan bambanta har a cikin gida.
Da yake fatan kwamitin nasa zai bude sabon babi na ci gaba a jam’iyar APC, Buni ya yi alkawarin yin sulhu na adalci tsakanin bangarorin da ke rikicin.
Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar ne ya kafa kwamitin Buni bayan rikicin shugabancin da ya haifar da bangarori biyu masu ikirarin shugabancin jam’iyyar.
Ya bukaci bangarorin da su amsa kiran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na janye karar da suka shigar domin jam’iyyar ta samu cigaba a sulhun da ake yi.
Ya ce, “A matsayin jam’iyyar siyasa mai akidu da mutane masu ka’idoji da mutunci, dole mu shirya wa sauye-sauyen da ke fata da kuma abin da za su haifar. Dole mu ne za mu yanke hukuncin irin sauyin da zai biyo baya a jam’iyyarmu.
Shugaban kwamitin rikon ya ce za su yi aiki cikin gaskiya da adalci da zai samu karbuwa ga duk bangarorin.
“Ayyukanmu a cikin watannin da ke tafe za su kasance ne ne riga-kafi ne ba na magani ba”, inji shi.