✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauye-sauyen da Majalisar Tarayya ta yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999

’Yan majalisa sun kada kuri’ar amincewa da wasu dokoki yayin da suka yi watsi da wasu.

A ranar Talata ’yan Majalisar Dokokin Tarayya da suka hada na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai suka fara kada kuri’a kan sauye-sauye 68 da aka gabatar na yi wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 kwaskwarima.

A zaman wanda Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa, Dolapo Osinbajo da Ministar Harkokin Mata, Paulen Talen suka halarta, ’yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da wasu dokoki yayin da suka yi watsi da wasu.

Aminiya ta rairayo wasu daga cikin sauyen-sauyen da suka samu shiga Kundin Tsarin Mulkin da wadanda suka yi bandaro bayan ’yan majalisar sun kada kuri’ar kin amincewa da su kamar haka:

  1. Majalisar Wakilai ta amince da kudirin wajabta wa yara samun ilimi kyauta. Hakazalika ilmi ya zama hakki na dukkan dan Najeriya.
  2. Majalisar Dattawa ta ki amincewa da kudirin kirkiro wa mata kujeru na musamman.
  3. Majalisar Wakilai ta ki amincewa da biyan fansho har zuwa lokacin mutuwa ga Shugabannin Majalisa.
  4. Majalisar Dattawa ta yi watsi da kudirin halasta zaman sauraron shari’a daga nesa ta hanyar bidiyo ko makamancin haka.
  5. Majalisar Wakilai ta amince da kudirin wajabta wa Shugaban kasa nada dan asalin Babban Birnin Kasar na Abuja a matsayin Ministan Abuja. Ta kuma amince da kudirin samar da Ofishin Magajin Garin Abuja.
  6. Majalisar Wakilai ta yi watsi da bukatar bai wa ’yan Najeriya mazauna ketare damar kada kuri’a a lokutan zabukan dake gudana a nan gida Najeriya.
  7. Majalisar Dattawa ta amince da kudirin bai wa Majalisa ikon umartar Shugaban Kasa ko Gwamna ya bayyana a gabanta.
  8. Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudirin sanya wa Shugabannin Majalisa da na Hukumomin Shari’a rigar kariya kamar yadda take a kan Shugaban Kasa da Gwamnoni.
  9. Majalisun biyu sun amince da kudirin bai wa Majalisun Dokoki na Jiha da Kananan Hukumomi da Hukumomin Shari’a yancin cin gashin kansu a kan duk wata harkalla ta kudi.
  10. Majalisar Wakilai ta yi watsi da dokar da za ta bai wa majalisa damar zagaye Shugaban Kasa tare da yin gaban kanta idan ya ki amincewa da wata doka.