✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauye-sauyen aiki a Masarautar Ingila saboda jinyar Sarki Charles III

Me zai faru idan ta kasance Sarkin ba zai iya aiki ba?

A sakamakon rashin lafiyar da Sarki Charles na Ingila, rahotanni daga kafofin yada labaran Birtaniya sun bayyana cewar ‘dan sa Yarima William mai shekaru 41 zai karbi ragamar tafiyar da wasu ayyukan mahaifin nasa.

Haka kuma, matarsa, Sarauniya Camilla za ta ci gaba da dawainiyar wasu nauye-nauyen da suka rataya a wuyan mijinta da ake jinyarsa.

Bayanai sun ce Sarkin ba zai so haka ba saboda zai so a ce ya halarci taron shugabbanin kasashe renon Ingila da za a yi nan gaba.

Ana saran Yarima William ya fara bayyana a bainar jama’a gobe Laraba, inda zai halarci bikin ba da kyaututtuka da kuma gidauniyar taimaka wa marasa galihu.

Rahotannin sun ce rashin kanin Sarkin, Yarima Andrew da dansa Yarima Harry na cikin harkokin gidan sarautar za su taikaita ayyukan da gidan zai dinga gudanarwa.

Shi dai Andrew ya janye daga harkokin da suka shafi fadar sarautar ne sakamakon rahotan dangantakarsa da Jeffrey Epstein mai cin zarafin mata, yayin da Harry, wanda shi ne karamin dan sarkin ya fice daga gidan sarautar domin kula da matarsa.

Fadar Buckingham ta ce yayin da Sarki Charles ke jinyar cutar kansa da aka tabbatar yana dauke da ita, zai ci gaba da gudanar da wasu ayyukan da suka shafi kasa da kuma gwamnati.

Tuni Firaminista Rishi Sunak da ya saba magana da Sarkin sau daya a kowanne mako ya sanar da cewar za su ci gaba da tuntubar da suka saba yi da Basaraken.

Kafofin yada labaran Birtaniya sun ce Sarkin ya ci gaba da karbar jajayen akwatunan da ke dauke da tarin takardun gwamnati kamar yadda ya saba kowacce safiya.

A ranar Litinin ce dai aka ruwaito cewa Sarkin Ingila, mai martaba Charles na III ya kamu da cutar kansa kamar yadda sakamakon binciken likitoci ya nuna.

Sanarwar da Fadar Buckingham ta fitar ta ce tuni ya fara karbar magani duk da cewa ba ta sanar da nau’in kansar da sarkin mai shekaru 75 ke fama da ita ba a yanzu.

Sai dai fadar ta ce, cutar ta kansa ba ta da alaka da maganin da aka yi wa sarkin na wata ‘yar karamar cutar mafitsara a kwana-kwanan nan.

A cewar fadar ta Buckingham, sarkin ya zabi ya bayyana sakamakon gwajin da aka yi masa ne ga jama’a domin hana yaduwar jita-jita, tare da fatan hakan zai taimaka wa al’umma su fahimci yanayin da mutanen da ke fama da kansa a sassan duniya ke ciki.

A cikin watan Satumban 2022 ne, Charles ya zama sarkin Ingila bayan mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth ta II ta mutu tana da shekaru 96.

Tuni manyan ’yan siyasar Birtaniya suka fara aikewa da sakon nuna goya baya ga sarkin na Ingila, inda suke fatan zai samu cikakkiyar murmurewa cikin kankanin lokaci.

Nauye-Nauyen da suka rataya a wuyan Sarki Charles III

Charles dai shi ne shugaban Birtaniya da kuma wasu kasashe 14 renon Ingila da ake kira Commonwealth ciki har da Canada da Australia da Jamaica.

Galibi dai hakikanin ayyukansa na al’ada ne kuma ba shi da hurumin shiga cikin muhawarar siyasa ba. Sai dai ana bukatar ya kafa dokokin Biritaniya, ya nada firaminista da bude zaman majalisa, da sauran ayyukan gudanar da mulki.

Sarki Charles wanda ya karbi ragamar mulki watanni 17 da suka gabata, ya karbi bakuncin shugabannin kasash.

Haka kuma, ya ziyarci wasu kasashen kamar Jamus, Faransa da kuma Kenya sannan ya gabatar da jawabi a Taron Sauyin Yanayi na COP28 da ake gudanar a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Me zai faru idan ta kasance Sarkin ba zai iya aiki ba?

Za a iya maye gurbin Sarki Charles da wasu mutum biyu da ke cikin sahun masu alhakin cin gajiyar gadon sarautar da ake kira Counsellors of State waɗanda ana iya zakulo su daga jerin da suka haɗa da sarauniya, magajinsa (William), da wasu ’yan uwa kamar ’yar uwarsa Anne ko ɗan uwansa Edward.