✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Saurin yanke hukunci’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Da fatan kuna cikin koshin  lafiya. A yau na kawo maku wani labari ne mai taken: ‘saurin yanke hukunci’. Labarin…

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Da fatan kuna cikin koshin  lafiya. A yau na kawo maku wani labari ne mai taken: ‘saurin yanke hukunci’. Labarin na kunshe da yadda mutane ke yanke hukunci akan abinda ba su da masaniya a kai. Da fatan Manyan Gobe za su kiyaye yanke hukunci ga abin da ba su da masaniya a kai. Asha karatu lafiya.

 

Akwai wani tsoho yana da yaro mai shekaru 25. Sai ya dauki dan suka shiga jirgin kasa. A bayan kujeransu akwai  wasu  mutane mata da miji.
Da jirgi ya fara tafiya, sai yaron ya sa hanunsa daya a kan tagar jirgi ya ce “Baba! Kalleni iska na hura ni”. Sai baban ya yi murmushi ya ce “da kyau”. Can sai yaron ya sake cewa “Baba! Kalli tsuntsaye akan bishiya” sai tsohon ya sake murmushi ya ce da shi “da kyau”. Can bayan mintuna kadan, sai aka fara yayyafi, sai yaron ya ce “la! Baba kalli ruwa na taba hannuna.
A wannan lokacin, halin yaron sai ya fara bai wa mutanen da ke cikin jirgin haushi. Ganin cewa ga shi ba karamin yaro ba kuma yana hali irin na yara. Sai daya daga cikinsu ya ce wa mahaifin yaron “don Allah ka yi wa danka magana domin yana damunmu kuma ba shi kadai ne a jirginnan ba. In da hali ka kai shi asibitin mahaukata don da alama ba shi da lafiya”. Sai mahaifin yaron ya yi murmushi ya ce da su “ dawowarmu kenan daga asibiti don tun da aka haife shi, sai yau ya fara gani kasancewarsa makaho”. Jin haka, sai jikin mutanen ya yi sanyi musamman ma wanda ya yi korafin..
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labarin. kuma ba za su zama masu saurin yanke hukunci ba a kan abin da suka gani.