✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saurayi da budurwa (2)

Wani saurayi ne ya je wajen budurwarsa suna tattaunawa kuma ga yadda hirarsu ta kasance: Saurayi: Ladidi an tashi lafiya?Budurwa: Ta yi shiru, ta ki…

Wani saurayi ne ya je wajen budurwarsa suna tattaunawa kuma ga yadda hirarsu ta kasance:

Saurayi: Ladidi an tashi lafiya?
Budurwa: Ta yi shiru, ta ki amsawa.
Saurayi: Ladidi, an kusa daura mana aure amma har yanzu ba ki daina yi mini wulakanci ba.
Babudurwa: Hummn, can maka dai!
Saurayi: Dama ba wani abu ne ya kawo ni ba illa in tambaye ki ko kin iya tuki. Domin ina son matata ta kware a tuki.
Budurwa: Hmmmn, Tanimu ke nan. Shi ya sa nake matukar son ka.
Saurayi: Hummm!
Budurwa: To wace irin mota za ka saya mini?
Saurayi: Mota kuma?
Budurwa: Eh mana, ba yanzu ka tambaye ni ko na iya tuki ba.
Saurayi: Tafdijam! Ni fa tukin tuwo nake nufi, domin kuwa buhun masara aka ba ni kyauta.
Daga Abubakar Malami