Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar Sudan na gab da rugujewa ganin yadda ake ci gaba da samun amon wuta da karar fashe fashe a birnin Khartoum, duk da tsawaita tsagaita wutar da bangarorin da ke rikicin kasar suka sanar a jiya.
Tuni wannan rikici wanda ya shiga mako na 3 ya tilasta wa dubban ’yan kasar Sudan tserewa zuwa kasashen makota irin su Masar da Chadi da kuma Jamhuriyar Afirka domin samun mafaka.
- Rikicin Sudan: Masar ta ba da lamunin ketarewa da daliban Najeriya
- Sojojin Turkiyya sun kashe shugaban IS Al-Qurashi
Akalla mutane sama da 500 aka tabbatar da mutuwar su a wannan rikici da ya barke tun daga ranar 15 ga watan jiya.
Ana dai barin wutar ne tsakanin Shugaban Sojin Sudan, Janar Abdel Fateh al-Burhan da mataimakin sa kuma shugaban jami’an tsaron kai dauki na RSF, Mohammed Hmadan Daglo.
Miliyoyin mazauna birnin Khartoum sun makale a cikin gidajen su yayin da suke fama da rashin abinci da kuma ruwan sha, yayin aka katse wutar lantarki, sai kuma jiragen yakin da ke ci gaba da shawagi suna kai hare hare ba tare da kaukautawa ba.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya ruwaito cewa ko a yau Litinin an ga jiragen yaki na shawagi a Kudancin birnin, yayin da mayakan Daglo ke kai musu hari da makaman kakkabo jirage.
Kasashen duniya kuma sun mayar da hankali ne wajen kwashe mutanen su da wannan rikici ya ritsa da su, yayin da alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna cewar ya zuwa yanzu an kwashe baki sama da 50,000.
Daliban Najeriya na cikin dubban ’yan kasashen waje da suke fatar ganin an mayar da su gida tun bayan barkewar rikicin, amma har ya zuwa wannan lokaci babu koda mutum guda da aka mayar gida.
Sai dai Babban Sakatare a Ma’aikatar Jin-kai ta Najeriya, Dokta Nasir Sani Gwarzo ya ce sun sake fasalin kwashe daliban, kuma yanzu za su yi amfani da tashar Port Sudan ne.
Ya zuwa yanzu iyayen wadannan dalibai na cikin zulumi ganin yadda yakin ke ci gaba da kazancewa, yayin da kasashen duniya suka kasa shawo kan hafsoshin da ke rikicin.