Wani rahoto ya bayyana cewa da yiwuwar sabuwar allurar rigakafin zazzabin cizon sauro da Jami’ar Oxford ta jagoranci samarwa ta iya tasiri wajen kawar da cutar daga ban kasa.
Yanzu haka gwaji ya tabbatar da cewa sabon rigakafin na Jami’ar Oxford na da tasirin kashi 77 wajen dakile cutar.
Wannan dai na zuwa ne bayan nau’in rigakafin Malaria da kamfanin magunguna na GSK ya samar a bara wanda kuma aka yi gwajinsa kan kananan yara fiye da miliyan guda a Afirka tare da tabbatar da tasirinsa wajen kariya daga cutar da akalla kashi 60.
Cutar ta Malaria wadda ke sahun cutuka masu hadari da kuma ke kisa babu kakkautawa, a 2020 kadai sai da ta kashe kananan yara dubu 627 galibi a nahiyar Afirka.
Nau’in rigakafin da jami’ar ta Oxford ta samar wanda aka sanya wa suna R21/Matrix-M shi ne na farko a tarihi da aka taba samarwa wanda ya zarta yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bukata wajen ganin duk wani magani da za a samar sai ya kai akalla kashi 75 wajen tasiri kan cutar ta Malaria.
An dai yi gwajin wannan magani kan yara 450 masu watanni 5 zuwa 17 a Burkina Faso inda Malaria ke haddasa mace-macen yara da akalla kashi 22 cikin 100.
A wannan shekarar dai an samu karancin mace-mace sanadiyyar zazzabin har a tsakiyar damuna bayan da aka bai wa yaran allurar rigakafin sau uku.