Saudiyya ta sanar da gagarumin aikin da za ta yi, ta amfani da tsuburai 50 don gina wurin shakatawa mafi girma a kasar, wanda za a gina a cikin tekun bahar maliya kamar yadda BBC ta ruwaito.
Saudiyya dai ta xauki wannan mataki ne domin jan hankalin masu yawon buxe ido daga sassa daban-daban na duniya, a kokkarin da kasar ke yi na rage dogaro ga man fetur da darajarsa ta karye a kasuwannin duniya.
Hukumomi sun ce za a rage tsauraran matakan da mutane ke fuskanta kafin samun bisar shiga kasar, inda wannan vangare na masu yawon buxe ido da shakatawa, za su samu cikin sauki.
Sai dai kawo yanzu ba a bayyana yanayin shigar da musu yawon buxe idon za su yi ba a kasar da ta zamo tushen addinin musulunci a duniya baki xaya.
Dama dai shan giya, da gidajen silima da na rawa haramtattu ne a kasar Saudiyya.
Haka kuma dole mata a kasar su suturce jikinsu, ta hanyar sanya suturar da ba matsattsiya ba, tare da rufe gashin kansu kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
A dokar kasar Saudiyya ba a amince mata su tuka mota ba, ko yin tafiya su kaxai ba tare da muharramansu ba.
A shekarar 2019 ne za a fara gabatar da aikin, inda za a fara da gina katafaren filin jirgin sama, da manyan otal-otal na alfarma, da gidaje ga masu sha’awar kamawa, kuma a shekarar 2022 ake sa ran kammala wannan aikin.
Wakilin BBC kan al’amuran kasashen labarawa ya ruwaito cewa ba bakon abu ba ne ga kasar Saudiyya, idan aka yi batun shiga da fitar baki, inda a duk shekara miliyoyin musulmai na tururuwa zuwa kasar mai tsarki don gudanar da ibada a lokutan aikin Hajji da Umarar watan azumin Ramadan da ke faruwa a duk shekara.
Sannan a sauran watanni 10 na shekarar kafa ba ta xaukewa ga masu ibadar, haka nan miliyoyin ma’aikata su ma na turuwa don gudanar da ayyuka.
Sai dai batun bin dokoki da ka’idojin da addinin musulunci ya shimfida a kasar, daga kan sanya sutura da rashin gudanar da harkokin shakatawa na daga cikin dalilan da masu yawon buxe ido ke xari-xari da ziyartar kasar.
Wannan dai wani vangare ne na kokarin da yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ya ke yi, wanda aka yi wa lakabi da ‘Muradun shekarar 2020’ ko ‘Vision 2020’ a turance. A kokarin karkatar da akalar yin ayyukan da kasar za ta samu kuxaxen shiga da nufin rage dogaro da man fetur da yawancin kasashen duniya suke yi, a daidai lokacin darajar xanyan mai ta ragu a kasuwannin duniya.
Haka nan buxe wurin na nufin samar da karin ayyukan yi ga ‘yan kasar, Sannan zai zamo aiki na farko ma fi girma da aka yi a kasar da ya danganci masu yawon buxe ido.
Cikin abubuwan da za a yi da za su janyo hankalin masu yawon buxe ido sun haxa da, dutsen da zai dinga zubo da ruwa, da wasu namun daji da ba kasafai ake samun su ba sai a kasashen labarawa, misali tsuntsun nan mai kama da shaho da sarakuna da attajiran larabawa ke amfani da su wajen farauta ko shakawatawa idan aka fita kilisa.
Masu yawon buxe idon za su samu damar kai ziyara rusasshiyar daular Madain Saleh, wurin da hukumar kula da kayan tarihi ta Majalisar Xinkin Duniya ta ayyana xaya daga cikin wuraren tarihi na duniya.