Gwamnatin Kasar Saudiyya ta ce za ta daukin nauyin karatun dalibai 424 daga Najeriya domin karantanr kwasa-kwasai daban-daban a jami’o’in kasar.
Wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Kasar da ke birnin Abuja ya fitar a ranar Litinin, ta ce daliban Najeriya da za a dauki nauyi na daga cikin guraben karatu 6,597 da aka tanada da za a rika rarraba wa daliban da suka fito daga kasashen nahiyyar Afrika duk shekara.
- An sayar da tattabara a kan miliyan N700
- An kama sigarin Dala 10m da aka yi fasakwauri a China
- Saudiyya za ta koma aiki da motoci masu amfani da lantarki
Sanarwar ta ce an kuma tanadi guraben karatu 150 da za a rika rarraba wa ga daliban da suka fito daga Jamhuriyyar Benin duk shekara.
Domin neman sanin ka’idodi da sharudan neman guraben karatun, an shawarci daliban da su nemi karin bayani daga Ma’aikatar Harkokin Waje da kuma Ma’aikatar Ilimi na kasashensu.
“Ana kuma iya samun karin bayani daga Ofishin Jakadancin Masarautar Saudiyya,” inji sanarwar.
“Ofishin jakadancin ya yaba da kyakkyawar dangartakar da ke tsakanin Masarautar Saudiyya da kuma Kasar Najeriya da sauran kasashen yankin Afrika da ta ke kawance da ita.”