Masarautar Saudiyya mai kula da Masallatan Harami ta yi bikin wanke Ka’abah da aka saba duk shekara bayan kammala aikin Hajji.
A madadin Sarki Salman bin Abdul Aziz al Saud, Yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman tare da Shugaban Masallatan Harami, Sheikh Abdul Rahman al-Sudays da kuma Limaman Masallatan Haramin ne suka jagorancin wankin Dakin Allah.
- ’Yan bindiga sun sace Kwamishina a Nasarawa
- Yadda rusasshiyar gada tsakanin Kano da Jigawa ta zama tarkon mutuwa
Shafin intanet na Haramain, wanda ya wallafa hotunan wankin Ka’abah, ya ce an gudanar da shi ne a safiyar Talatar nan.
Ana amfani ruwan zam-zam da turaruka masu kamshi, ciki har da miski da kuma tawul mai tsabta wajen wanke dakin Ka’abah.
Akan tanadi dukkan abubuwan da ake bukata kwana guda kafin a wanke dakin.
BBC ya ruwaito cewa, ana shafe sa’o’i biyu wajen wanke dakin.
Wanke dakin Ka’abah ya faro ne tun daga lokacin Annabi Muhammad (SAW).