Yarima mai jiran gadon Saudiyya Muhammad Bin Salman ya mayar da zazzafan martani ga masu sukar kasar kan kashe makudan kudade a harkokin wasanni da ma sayen ‘yan wasa.
A baya-bayan nan dai Saudiyya na zuba kudade na ban mamaki wajen farfado da gasar League din kasar tare da siyan zaratan ‘yan wasa kan kudade masu tarin yawa.
- An ceto wasu daga cikin daliban jami’ar da aka sace a Gusau
- Jamus ta naɗa Julian Nagelsmann kociyan tawagar ƙasar
To sai dai tuni kungiyoyi musamman na kare hakkin dan Adam suka fara sukar yariman, yayin da suke ganin wannan sam barnar kudi ne a kasar da a cewarsu hakkin dan Adam ba shi da wata kima.
Yayin da ya ke zantawa da gidan talabijin na Fox, Yarima Salman, ya ce idan kashe tsabar kudi wajen farfado da gasar League din kasar zai daga darajar tattalin arzikin Saudiyya da kaso daya tak, to ba shakka zai ci gaba da haka.
Yariman ya ce duk ma abin da masu suka za su kira yunkurin nasa su kira, amma matukar hakan zai tasiri ga tattalin arzikin Saudiyya, to kuwa babu abin da zai dakatar da shi.
Tun a tsakiyar kakar bara da fitaccen dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo ya koma kasar Saudiyya da taka leda bayan ya raba gari da Manchester United, sai gasar kasar ta kara armashi a idon masoya kwallo.
Duk da cewa fitattun tashoshin talabijin da suke nuna wasannin kwallon kafa na duniya ba sa nuna gasar ta Saudiyya, masoya dan wasan da ma wadanda ba sa son shi, suna bibiyar kafar YouTube domin ganin yadda take kayawa da shi da Kungiyar Al Nassr da ya koma da wasa.
Kawo yanzu akwai fitattun manyan ’yan wasa da suka bi sahun Ronaldo ciki har da Neymar, Ruben Neves, Edouardo Mendy, N’golo Kante, Karim Benzema, Kalidou Koulibaly da sauransu.