✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta yi wa Messi tayin ninkin albashin Ronaldo

Idan ta tabbata, Messi zai zama dan wasa mafi albashi a duniya

Kungiyoyin kwallon kafa a kasar Saudiyya na zawarcin gwarzon dan wasan duniya, Lionel Messi, na kungiyar PSG, da tayin albashin da ya zarce na kowane dan wasa a duniya.

Rahotanni sun nuna cewa wata kungiya da ke zawarcin Messi a Saudiyya ta yi masa tayin albashin Naira biliyan 183.5 (Dala miliyan 400) a shekara, idan kwantaraginsa ya kare da PSG a wata mai zuwa.

Kafar labarai ta Telegraph ta kasar Birtaniya ta ce dan wasan ya fara tunanin duba tayin kuma tuni kungiyar ta fara tattaunawa da Kyaftin din na kasar Argentina kan kwangilar da take masa tayi, bayan dakatarwar da PSG ta yi masa.

Idan hakan ta tabbata, Messi zai rika karbar kusan ninki biyun albashin babban abokin hamayarsa Cristiano Ronaldo, wanda a halin yanzu Al Nassr ta kasar Saudiyya ke biyan sa Naira biliyan 96.3 Dala miliyan 210 a shekara, zuwa 2025.

A halin yanzu dai, Cristiano Ronaldo ne dan wasa mafi albashi a duniya, inda Messi ke biye da shi, kafin Kylian Mbappe na Farasan da PSG.

Wannan sabuwar ta taso ne bayan da kungiyar PSG ta dakatar da Messi na tsawon mako biyu ba tare da albashi ba, saboda wata ziyara da ya kai Saudiyya ba da izinin kungiyar ba.

A baya dai an yi ta rade-radin kungiyar Al Hilal ta Saudiyya ce ke neman daukar Messi, daga baya da PSG ta takatar da shi kuma maganar ta kara tasowa.

A cikin makon nan ne dai dai Saudiyya ta ayyana Messi a matsayin jakadarta na tallata harkokin yawon bude ido, a wani bangare na kwatarangin nasa, kamar yadda aka ruwaito.