✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta kayyade wa alhazai lokacin jifa saboda tsananin zafi

An ba da wannan umarnin ne sakamakon tsananin zafi da ake tunanin ya yi ajalin wasu alhazai a ranar Lahadi

Gwamnatin Saudiyya ta ba da umanrin hana alhazai fita zuwa wurin jifa daga karfe 11 na safe zuwa 4 na yamma agogon kasar.

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta ba da wannan umarnin ne sakamakon tsananin zafi da ake tunanin ya yi ajalin wasu alhazai a ranar Lahadi — ranar jifan farko.

Sanarwar da aka tura wa hukumomin aikin hajji na kasashen duniya ta kara da cewa ma’aikatar ta umarci jami’an tsaro da su dakatar da alhazan da suka bijire wa wannan umarni.

Aikin Hajjin bana, kamar na sauran shekarun baya, ya gudana ne a cikin yanayi na tsananin zafi inda zafin rana kan haura maki 40.

Hukumomin hajji da na lafiya sun yi ta jan hankali alhazai da su yaiwa shan ruwa da amfani da lema da kuma gujewa shiga rana a yayin ibadar aikin Hajji da ma zamansu a Saudiyya.

A halin da ake ciki alhazai suna a sansanin Mina inda za su ci gaba da yin jifa zuwa ranar alata ko Laraba a matsayin wani bangare na aikin Hajji.

Ana fara jifa a ranakun jifa – 10 zuwa 13 ga watan Dhul-Hajji – ne daga lokacin hantsi zuwa faduwar rana.

Akasari a kafa ake zuwa da dawowa daga wurin jifan, wanda ke da tazarar kimanin kilomita biyar daga tantunan alhazan Najeriya.