✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya da Iran za su ci gaba da huldar diflomasiyya bayan shekara 6 da yanke alaka

Saudiyya ta yanke dangantaka da Iran ne a 2016.

Iran ta ce Saudiyya ta gayyaci shugaban kasar Ebrahim Raisi domin zuwa wata ziyara a kasar – mako daya tun bayan da kasashen biyu suka amince su ci gaba da huldar diflomasiyya.

An bayyana cewa batun gayyatar na kunshe ne cikin wata wasika da Sarki Salman ya rubuta, sai dai ’yan kasar basu tabbatar da hakan ba.

Kasashen biyu da ke yankin Gabas ta Tsakiya, sun yi ta samun takun-tsaka na tsawon shekaru.

China tana cikin kasashen da suka shiga tsakani wajen ganin kasashen sun dawo dasawa, abu kuma da aka bayyana cewa zai sauya siyasar yankin.

Wani babban jami’in gwamnatin Iran, Mohammad Jamshidi, ya wallafa a shafinsa a Twitter kan batun ziyarar zuwa Saudiyya, inda ya ce Mista Raisi ya yi maraba da batun da kuma nanata cewa Iran na da zummar fadada dangantaka.

Shi ma, Ministan Harkokin Wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya fada wa manema labarai cewa kasashen biyu sun amince su yi zama a matakin ministocin harkokin waje, inda ya ce an tsara gudanar da zaman ne a wurare guda uku.

Sai dai bai bayyana sunayen wuraren ba, ko kuma sanar da ranar da za a yi zaman ba.

BBC ya ruwaito cewa, wannan ci gaba da aka samu a dangantaka tsakanin kasashen biyu a baya-bayan nan wanda China ta shiga tsakani, na kara kyautata al’amura.

Kasashen sun sanar da cewa za su sake bude ofisoshin jakadancinsu nan da wata biyu da sake karfafa huldar kasuwanci da kuma na tsaro.

Kasashe da dama sun yi na’am da wannan ci gaba da aka samu, ciki har da Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya, bayan yunkurin sulhunta kasashen a baya ya ci tura.

Saudiyya ta yanke dangantaka da Iran ne a 2016 bayan da masu zanga-zanga suka afka wa ofishin jakadancinta a Tehran.