✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiya da Qatar sun koka kan rashin kulawa da rikicin Gabas ta Tsakiya

Manyan kasashen duniya ba su taba jajircewa wajen kawo karshen tashin hankalin da ake fama da su a Gabas ta Tsakiya ba.

Saudiya da Qatar sun bayyana bacin ransu kan rashin kulawa da rikicin Gabas ta Tsakiya da manyan kasashen duniya ke yi, a daidai lokacin da kasashen yammacin Turai ke matsa musu lamba kan su nuna goyon baya ga Ukraine da Rasha ta mamaye.

Bayanai sun ce Ministan Harkokin Wajen kasar Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al- Thani ne ya yi tsokaci kan lamarin yayin bude wani wani taro a birnin Doha ranar Asabar.

Ya ce tashin hankali da tagayyarar mutanen da ake gani a Ukraine, da kowa ke magana a kai, an dade ana ganin makamantansu da ma wadanda suka zarce na yanzu a kasance kasashe da dama na yankin Gabas ta Tsakiya tsawon shekaru, kuma babu abin da ya faru.

A cewar ministan na Qatar, manyan kasashen duniya ba su taba jajircewa wajen kawo karshen tashin hankalin da al’ummar Syria, ko na Falasdinawa da ’yan Libya, da ’yan Iraqi, ko kuma ’yan Afganistan da ’yan Yemen ke ciki ba, kamar yadda suka tashi tsaye kan halin da Ukraine ta shiga bayan mamaye ta da Rasha ta yi.

Saudiyya mai arzikin man fetur ko kuma Qatar mai arzikin iskar gas, dukkansu kawaye ne ga kasashen Yammacin Turai, sai dai har yanzu basu bayyana wani matsayi kwakkwara ba wajen caccakar yakin da Rasha ke yi a Ukriane, saboda alakar kusancin da ke tsakaninsu.

Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa Turai da Amurka na fatan kasashen biyu za su kara habaka samar da mai da iskar gas don taimakawa wajen rage dogaron da kasashen yammacin Turai ke yi kan kayayyakin Rasha.