Terry Ikponmwosa, wani matashi mai kimanin shekaru 31 a duniya ya bayyana yadda masu safarar mutane suka sayar da shi har sau hudu kafin ya karasa kasar Libya a kokarinsa na tsallakawa Tura domin samun sabuwar rayuwa.
A tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a birnin Benin na jihar Edo ranar Juma’a, ya ce kusan bautar da shi kawai aka yi kafin ma ya ankara.
Ya ce, “Bayan na kammala karatuna na sakandire, sai na fara kasuwanci. Na bude wurin sayar da siminti, kuma ina ciniki sosai, ina samun kudi, amma sai na ji ina bukatar wadanda suka fi haka.
“Lokacin da nake harkar simintin, sai wani abokina ya hada ni da wani mutum a Benin wanda ya yi alkawarin taimaka min na tafi Turai.
“Ina da jarin sama da Naira miliyan daya, amma haka na tarkata su na bashi saboda buri na ya cika.
“Na bar shagon a hannun wani aboki na don ya rika ba iyali na kudin hayar wurin su ci gaba da kula da kansu, amma sai ya sayar ya gudu da kudin.
“Ashe ni ban ma sani ba hannun mai safarar mutane na fada kuma tuni ma ya sayar da ni ga wani mutum a garin Agbor na jihar Delta.
“Bayan sa saye ni, sai shi ma ya sayar da ni a cikin garin dai na Agbor. Daga nan sai aka sake sayar da ni ga wani mutum a Kano. Duk sun yi hakan ne ta hanyar fakewa da cewa za su hada ni da wanda zai yi min jagora a tafiyar cikin sauki.
“Ashe tuni ma masu cinikin har sun ma riga sun sayar da ni a Libya tun ma kafin na karasa.
“Mu 36 ne muka bar Kano muka kama hanyar Libya, amma mu hudu ne kacal muka kai, ragowar duk mutuwa suka yi a Sahara saboda kishin ruwa da yunwa.
“Sai dai na yi rashin sa’a, a kokarina na tafiya Turai an kama ni tare da wasu ’yan Najeriya aka kai mu kurkuku.
“A cikin kurkukun ne ma na yi nadamar fara tafiyar tun da farko saboda babu komai a cikinta face wahala da bacin rai,” Inji shi.
Ikponmwosa ya ce a cikin kurkukun ne ya yanke shawarar komawa yin azumi da addu’o’in neman mafita, kafin daga bisani Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa da Kasa ta kawo musu dauki.
Ya ce bayan dawowarsa Najeriya ne ya hadu da mutumin da ya fara sayar da shi a Benin amma ya nemi gafararsa tare da alkawarin dawo masa da dukkan kudaden da ya kashe.
“Daga karshe da na yanke shawarar kai shi wurin Kwamitin Yaki da Safarar Mutane na jihar Edo domin ya biya ni kudi na, sai ya gudu ya bar jihar gaba daya,” inji shi.
Ya ce yana da muhimmanci a ilimantar da mutane musamman matasa a kan illar dake tattare da irin wannan tafiyar.
Ikponmwosa ya kuma shawarci ’yan Najeriya da su bi hanyoyin da suka dace domin irin wadannan tafiye-tafiyen don gudun fadawa makamancin halin da ya shiga.
“Yana da kyau a lura cewa tafiya ta Sahara na iya kaiwa ga rasa rayuwar mutum ko dai a cikin Saharar ko kuma a kogin Mediterranean, ko ta bautarwa, daurewa a kurkuku, ko kuma ta hanyar tilasta mutum yin aikin karfi.
“Ba zan iya musalta abubuwan da na gani a Sahara da Libya ba, duk lokacin da na tuna sai na zubar da hawaye. Ba na fatan kowa ya fada cikin irin wanann yanayin,” inji shi.