Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari Abubakar ya ce Sarkin Zurmi ya taba ce masa ya sa a shafe kauyen Dumburun da ke jihar bayan da ya zargi daukacin mutanen kauyen da kasancewa ’yan bindiga ko masu boye su.
Gwamna Yari ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi wani kwamitin mutum bakwai da aka kafa don binciken harin da ake zargin sojin sama sun kai kan fararen hula a jihar a yakin da suke yi da ’yan bindiga, lokacin da kwamitin ya ziyarci Gwamnan a gidansa da ke Talatan Mafara.
Gwamna Yari Abubakar ya ce kauyen Dumburum ya zama mafakar ’yan bindiga a cikin shekara uku da suka wuce.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito Gwamnan yana cewa ba zai nemi gafara kan harin da sojojin suka kai ba, inda ya ce: “A matsayina na shugaba a jihar, ina ganin Rundunar Sojin Saman Najeriya ba ta aikata ba daidai ba, kuma ba wani bayani da aka yi min dangane da harin.”
Ya ce “A cikin shekara uku da suka wuce garin Dumburum, ya kasance matattarar ’yan bindiga. Kuma ko shi Sarkin Zurmin kansa, ya taba neman in shafe kauyen, saboda yana ganin dukkan mazauna kauyen ’yan bindiga ne. Don haka, na ji mamaki da Sarkin Zurmi yake cikin masu cewa, an hallaka fararen hula a yankin.”
Kamfanin NAN, ya ruwaito Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara tana zargin cewa wadanda farmakin saman ya rutsa da su a yankin da cewa mutane ne da ba su ji ba ba su gani ba.
Gwamna Yari ya ce da akwai wadansu gaggan mutane da ke yi wa jihar yankan baya, inda ya ce “Da akwai wadansu mutane, suna zaune a Abuja, amma suna ta yada shaci-fadi marar tushe, kawai don su bata yakin da ake yi da ’yan bindigar. Ba za mu taba lamunce wa haka ba.”
“Ina kira ga dukkan jami’an tsaro, musamman Rundunar Mayakan Sama, ku ci gaba da gudanar da ayyukanku bisa doka, kuma Gwamnatin Jihar Zamfara, a shirye take wajen ba ku duk goyon bayan da kuke bukata, a kokarinku na maido da zaman lafiya a jihar, wanda aka rasa tun shekarar 2007,” inji Gwamnan.
“Ku ci gaba da nuna kwazonku don nuna wa ’yan bindigar cewa akwai gwamnati. Ba za mu sake hawa teburin sulhu da su ba, saboda a baya mun yi hakan; sai shugabanninsu suka yi ta yi mana fuska biyu; a zahiri komai na tafiya daidai, alhali kuwa sun bar yaransu na kaddamar da hare-hare a kan jama’a,” inji shi.
Da yake mika takaddar ta’aziyar Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Marshal Saddikue Abubakar, jagoran ayarin, Iya Bayis Mashal Idi Lubo, ya ce hakan nuna alhini tare da damuwar da Babba Hafsan Mayakan Saman ke yi, idan har zargin kashe fararen hular ya tabbata.
Iya Mashal Lubo ya kara da cewa: “Babban Hafsan Mayakan Saman ya umarce mu da gudanar da kwakkwaran bincike a kan zargin, don gano ainihin abin da ya faru. Mun ziyarci masu ruwa- da-tsaki a kan batun, kuma mun gano cewa akwai matsalar rashin fahimtar juna a yada labarin. Don haka, muna tabbatar wa al’ummomin yankin cewa za mu ci gaba da gudanar da aikacen-aikacenmu na kare rayuka da dukiyon jama’a bisa nuna kwarewa da sanin makamar aiki.”
Kwamandan Sojin kai daukin ta 207, Sukwardiron-Lida Sunkanmi Thomas wanda ya zagaya da ayarin, ya gode wa dukkan masu ruwa-da-tsaki kan goyon bayan da suke bai wa ayyukan mayakan saman a Jihar Zamfara.