✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau ya tumbuke rawanin Ciroman Zazzau

An sauke Ciroman saboda rashin biyayya da kuma sukar asalin Sarki Bamalli

Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya tube rawanin Ciroman Zazzau Alhaji Sai’du Mai Lafiya.

Sarkin ya sauke Ciroman mai shekara 84 ne bisa zargin rashin biyayya ga Masarautar, kuma tuni ya maye gurbinsa da Barden Zazzau kuma Hakimin Makera, Alhaji Shehu Tijani Aliyu Dan Sidi.

Wata majiya daga cikin fadar ta bayyana cewa Ciroman ya kasance marar biyayya ga Sarkin tun lokacin da aka nada shi. “Kusan sau shida Ciroman yana nuna rashin biyayya tare da tozarci a gaban ’yan Majalisar Sarki.

“Ana kuma zargin sa da kokarin tunzura ’yan uwanshi na tsatson gidan Mallawa domin su yi wa Sarkin bore,” inji majiyar.

Ta ce tubabben Ciroman ya kuma kalubalanci asalin Sarkin na Zazzau, inda har yake masa gori da cewa dan gidan wanzamai ne.

Tubabben Ciroman Zazzau din na daga cikin manyan ’Yan Majalisar Sarki kuma Dan uwa na kusa ne ga Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli.

A halin yanzu, Ciromon shi ne kusan babba a jerin ’ya’yan sarki da suka fito daga gidan sarautar Mallawa a Masarautar Zazzau.