✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau jigon hada kan al’umma ne —Tambuwal

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana Sarkin Zazzau, marigayi Alhaji Shehu Idris a matsayin jigon hada kan al’umma. Tambuwal ya bayyana haka a…

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana Sarkin Zazzau, marigayi Alhaji Shehu Idris a matsayin jigon hada kan al’umma.

Tambuwal ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziya ga iyalai da kuma jama’ar kasar Zazzau a safiyar Litinin.

“Ba kasar Zazzau ba ce kawai ta yi rashi; ko su da suka san Mai Martaba Sarkin Zazzau daga baya sun san cewa uba ne mai son zaman lafiya.

“Ya kuma iya tafiyar da mulki, don haka muna fatan Allah Ya yi mishi rahama”, inji Gwamna Tambuwal.

Gwamnan wanda ya jagoranci tawagar jihar Sakkwato cikinsu har da tsohon gwamnan jihar, Satana Aliyu Magatakarda Wamakko da kuma tsohon dan majalisan tarayya Jawo Sumaila.