✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau a Sallar Juma’ar farko bayan nadi

Dubban jama'a sun taru domin ganin Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli a Sallar Juma'arsa ta farko

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya halarci Sallar Juma’a ta farko bayan ya hau karagar mulki.

Sarki Ahmed Bamalli wanda aka nada a ranar Laraba 7 ga Oktoba 2020 na halartar Sallar ne a Masallacin Fadarsa da ke Zariya.

Dubban mabiya sun yi cincirindo domin dagin Sarkin lokacin sallar jama’ar.

A ranar Alhamis masu zabar Sarki da kuma gidajen Sarauta na Masarautar Zazzau suka yi mubaya’a ga sarkin.

Zuwa Sallar Juma’ar ita ce fitar Sarkin ta farko tun bayan nada shi a ranar 7 ga Oktoba, 2020.
Yaddda jama’a suka yi taro domin ganin Sarkin bayan idar da sallar Juma’a
Wasu daga mutanen da suka taru a fadar sarkin domin ganin sa ranar Juma’a
Masu kallo Sarkin Zazzau a fadarsa da ke Zariya.

Ahmed Bamalli shi ne Sarkin Zazzau na 19, wanda kuma ya gaji surukinsa, Sarki Shehu Idris, wanda ya yi mulki na tsawon shekara 45 kafin Allah Ya yi masa rasuwa.

Kafin zamansa Sarki, Ahmed Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kuma ya fito ne daga gidan Mallawa, daya daga cikin gidaje hudu masu sarautar Zazzau.