Sarkin Kauran Namoda, Mai Martaba Sanusi Muhammad Asha, ya tsallake rijiya da baya bayan ’yan bindiga sun kai masa hari.
’Yan bindiga sun hallaka ’yan sanda uku da wasu mutum biyar a harin da suka kai wa tawagar motocin Sarkin a kan hanyar Zariya zuwa Funtua a Jihar Katsina.
- Daliban Kankara sun sauka a Gidan Gwamnatin Katsina
- Yadda muka sasanta aka sako Daliban Kankara ba biyan kudin fansa
Sarkin da iyalinsa na hanyarsa ta komawa gida daga Abuja ne da dare lokacin da ’yan bindiga suka far masa.
Maharan sun yi ruwan wuta babu kakkautawa a kan wata mota kirar Hilux da ke cikin ayarin motocin Sarkin Kaura Namoda.
Nan take suka aika ’yan sanda uku lahira tare da wani kawun sarkin wanda aka bayyana da Dan Amal sai wani babban dogarin sarkin da kuma karin wasu mutun biyu da harin ya yi ajalinsu.
Kwamishin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Zamfara, Usman Nagogo, ya tabbatar da harin, sai dai bai yi karin haske a kai ba.
Basaraken da matarsa sun aun arzikin tsallake rijiya da baya a harin na ranar Alhamis, ranar da ’yan bindiga suka sako dalibai 344 da suka yi garkuwa da su a makarantar GSSS Kankara a Jihar.
Kafin zamansa Sarkin Kaura Namoda, Alhaji Sanusi, hafsan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ne mai mukamin Manjo.