Allah Ya yi wa Sarkin Kaura Namoda da ke jihar Zamfara, wanda aka fi sani da Sarkin Kiyawan Kaura Namoda, Ahmad Muhammad Asha, rasuwa.
Sarkin ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi yana da shekara 71.
Dan uwan marigayin, wanda kuma shi ne Dan Jekan Kaura Namoda, Abdulkarim Ahmad Asha, ya tabbatar wa Aminiya lamarin yana mai cewa Sarkin ya rasu ne bayan ya yi jinyar ciwon suga da hawan jini na tsawan lokaci.
“A lokacin da ciwon ya taso masa ya yi kwanaki hudu yana fama, kafin daga bisani a kai shi Asibitin Kwararru na Yariman Bakura; bayan ya yi kwanaki uku a asibitin ya rasu,” inji Dan Jekan Kauran Namoda.
- Sarkin Rano ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya
- Farfesa Isa Hashim: Kano ta sake babban rashi
- Coronavirus: Ana neman wani ‘majinyaci’ ruwa a jallo a Zamfara
Sarkin ya rike mukamin darakta a sashen kudi na wasu kananan hukumomin jihar, ciki har da Kaura Namoda da Gusau da Maru kafin a nada shi sarki a shekarar 2004.
“Marigayin ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya 11; a cikin ’ya’yansa akwai Sanusi Muhammad Asha wanda ke aiki da rundunar sojojin Najeriya a Maiduguri babban birnin jihar Borno.”
An shirya binne shi a garin Kaura Namoda kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.