✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Katsina ya yi taro da kungiyoyi don zaman lafiya

A yau Alhamis ne Mai martaba Katsina Sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir, ya yi taro da hadaddun kungiyoyin zaman lafiya da ke cikin masarautarsa a…

A yau Alhamis ne Mai martaba Katsina Sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir, ya yi taro da hadaddun kungiyoyin zaman lafiya da ke cikin masarautarsa a dakin taro na hukumar kula da Kananan Hukumomin jihar Katsina.

Mai martaba Sarkin ya ja hankali musamman iyaye mata a kan kula da ƴaƴansu musamman ta fannin batun yawan tallace-tallace a tituna wanda hakan ke jefa su cikin matsaloli.

Kazalika, Sarkin ya yi kira ga sauran iyaye maza wadanda sune ke daukar nauyin ke kansu tare da kulawa a kan yadda ake barin matasa na shiga cikin matsalar shaye-shaye wanda hakan ke janyo bala’o’i iri-iri a cikin kasa. A kan haka, ya ce nauyin zaman lafiya ya rataya a kan kowa domin babu wanda baya son zaman lafiyar.

Sarkin wanda ya yi jawabi mai tsawo, ya janyo hankalin jami’an tsaro, ƴan jaridu da sauran duk wani mai ruwa da tsaki a kan abin da ya shafi tsaro na fannoni daban-daban.

Shi kuwa shugaban Kwamitin Alhaji Bilya Sanda cewa ya yi, daga cikin bincike da kuma abubuwan da suka gano su ne, shigowar baki. Hakan yasa dole, sai an shigo da masu sana’ar acaba ko masu sana’ar tukin babur mai kafa uku (Kake NAPEP), domin da su ne ake amfani wajen shiga kowace irin unguwa ko sako.

Kazalika, shugaban kwamitin ya ce, sun bayar da shawarar bullo da wadannan kwamitoci irin na Shari’a, Da’awa, Tsaro, kwamitin kula da saye da sayar da gidaje ciki har da bayar da haya ko fili.

Kwamitin kula da mata da matasa, sai na kula da tsare-tsare da kididdiga.

Shi wannan kwamiti na zaman lafiya daga masarautar ta Katsina zai ci gaba da gudana tare da aiwatar da aiyukansa wanda zai shafi kowa ne bangare na rayuwar al’umma.

Mahalarta taron