✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Jere Sa’ad Usman ya rasu

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Jere da ke Jihar Kaduna, Dokta Sa’ad Usman, rasuwa bayan ya sha fama da rashin lafiya sakamakon raunin…

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Jere da ke Jihar Kaduna, Dokta Sa’ad Usman, rasuwa bayan ya sha fama da rashin lafiya sakamakon raunin da ya yi yayin wani rikici a yankin.

Kanin marigayin, Aminu Jere, shi ya sanar da rasuwar Sarkin.

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun. Yanzun nan na yi rashin dan uwana Sarkin Jere, Dokta Sa’ad Usman”, inji Aminu, wanda ya kara da cewa, “Za a yi sallar janazah a garin Jere da karfe 2.00 na rana”.

Marigayin dai miji ne ga tsohuwar Ministar Kudi a zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, kuma tsohuwar ’yar Majalisar Dattawa, Esther Nenadi Usman.

Ya kuma taba rike manyan mukamai a gwamnatin Jihar Kaduna, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jiha.