✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Jama’a ya yaba wa cibiyar sauraron koke-koke

Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya yaba wa Cibiyar Sauraron Koke-Koke ta Salama da ke da ofishi a Babban Asibitin Kafanchan…

Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya yaba wa Cibiyar Sauraron Koke-Koke ta Salama da ke da ofishi a Babban Asibitin Kafanchan bisa kokarin da take yi wajen dakile aukuwar ayyukan da suka shafi cin zarafi da musgunawa da sauran ayyuka dangin fyade ta hanyar daukar matakan shari’a ga wadanda aka kama da kuma bayar da kula ga wadanda aka yi, inda ya nuna goyon bayansa kan wannan yunkuri.

Sarkin Jama’a, ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar bakuncin wakilan cibiyar da suka kawo masa ziyarar ban-girma a fadarsa da ke Kafanchan.

“Yanzun kanun labaran da ya cika kafofin watsa labarai ke nan na musguna wa kananan yara da sauransu. Don haka wannan yunkuri ne mai kyau,” inji shi.

A lokacin da take jawabi, Shugabar Cibiyar Misis Grace Yohanna Abbin ta mika godiyarta ga Masarautar Jama’a da cibiyar ke yankinta, inda ta bayyana farin cikinsu ga irin goyon bayan da ake ba su.

Da take karin haske game da cibiyar, Misis Abbin ta ce gwamnatin jihar ce ta samar da wurin kuma babu kudin da ake karba daga duk wanda ya kawo kokensa, don haka ta yi kira ga jama’a su saki jikinsu su kawo kokensu ko na wadansu da suka ga ana musguna musu ko ana keta hakkinsu domin cibiyar na da ma’aikata da suka hada da likita da nas da mashawarci na musamman sannan suna da hadin gwiwa da jami’an tsaro.

“Baya ga nan muna da lauyoyi koda ta kama a kai wanda ake tuhuma kotu ne mukan bai wa mutum lauya kyauta don ya tsaya masa wajen kwatar masa hakkinsa,” inji ta