✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Hausawan Abekuta ya nada sabon Sarkin Guragu

A kwanakin baya ne fadar mai martaba sarkin Hausawan Abekuta, Alhaji Ibrahim Hassan Hassan ta cika maƙil da nakasassun da suka hada da gurugu da…

A kwanakin baya ne fadar mai martaba sarkin Hausawan Abekuta, Alhaji Ibrahim Hassan Hassan ta cika maƙil da nakasassun da suka hada da gurugu da makafi, waɗanda suka taho daga jihohin Legas da Ogun da Oyo da wasu jihohin Arewa domin shaida sararutar sarkin guragun Abekuta, Malam Idris Sa’adu Warawa.

Sarkin na Hausawan Abeokuta ya shaida wa Aminiya cewa ya nada sarkin guragun ne domin ya jagoranci jama’arsa naƙasassu, domin sukan fuskanci matsaloli game da su, don haka sarkin guragun ya cancanta ya yi masu jagoranci ya kuma ɗora su bisa turbar bin dokokin gwamnatin jihar dangane da abin da ya shafi sana’arsu ta bara. “Gwamnan jiharmu Sanata Ibikunle Amusun ba ya son ya ga mabarata na yawo bisa manyan tituna, don haka ne ya gina masu waje na musamman a kasuwar Lafenwa, ya killace su a nan, sannan ya yi shellar cewa duk mai niyyar ba da sadaka ya kawo ta nan rumfar tasu. A kan haka ake a yanzu, don haka ne muka ga ya dace mu naɗa sarkin guragun da zai taimaka mana wajan ganin an bi dokar da gwamnati ta kafa,” inji shi.

Malam Idris Sa’adu Warawa ya sami sarautar ne bayan da tsohon sarkin guragun Abeokutan ya yi ƙaura zuwa garin Ijebu Ode kafin daga bisani ya koma garin Ore, a jihar Osun. Sabon sarkin guragun ya shaida wa Aminiya cewa cewa duk da cewa su jama’a ne masu rauni, zai yi duk abin da ya dace domin samun haɗin kan ɗaukacin jama’arsa da makafi da shuwagabanni na sama da su, da zimmar samun daidaito da bin dokar gwamnati a lokacin da suke gudanar da harkokinsu a jihar. “Wannan rana ce da na daɗe ina jira, sai ga shi Allah Ya tabbatar mana. Ina matuƙar godiya a gare shi, da fatan Allah Ya saka wa duk jama’ar da suka zo domin taya ni murna,” inji shi.

Shi dai sabon sarkin guragun, Bafulatani ne ɗan asalin garin Geza, karamar Hukumar Warawa a Jihar Kano. Ya kuma shafe sama da shekara 40 a Kurmi, inda ya zauna a Jihar Legas kafin daga bisani ya koma garin Abekuta da zama. 

Bikin nadin sarautar ya sami halartar sarkin Fulanin Abekuta da sarkin guragun Alabgado da na guragun Ibadan da na garin Shagamu da wakilin sarkin guragun Ifo.