Sarkin Anka kuma Shugaban Majalisar Sarakuna na jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad Anka, ya musanta batun da ake alakanta shi da shi cewa ya kuduri aniyar kawo cikas a kokarin da gwamna Bello Matawalle yake na tabbatar da zaman lafiya a jihar Zamfara.
Cikin fushi da kakkausar murya ya mayar da martani kan kalaman da gwamnan matawalle ya furta kan zarginsa na kokarin dakile shirinsa na tabbatar da zaman lafiyar jihar da yaki da ’yan ta’adda musamman garkuwa da mutane.
- Gobara ta tashi a masana’antar rigakafin COVID-19
- Mutum 3 sun gurfana a gaban kotu kan laifin tayar da zaune tsaye
Sarkin ya ce, ’Yan jarida ne suka yi kuskuren nakalto ainihin abin da ya furta, ya kuma jaddada cewa shi ko kadan bashi da manufar dakile shirin gwamnatin na tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ya ce, “Ni mamba ne a Kwamitin samar da zaman lafiya a jiha kuma ni ban fadi wani abu makamancin wannan ba wanda yana da kyau a koma a saurari ainihin abin da na fada tunda farko” cewar Sarkin.