✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki Sanusi II ya samu ‘yanci zai bar garin Awe

Tubabben Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya samu ‘yanci a yanzu haka yana shirin fita daga garin Awe da ke jihar Nasarawa. An dai kai…

Tubabben Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya samu ‘yanci a yanzu haka yana shirin fita daga garin Awe da ke jihar Nasarawa.

An dai kai tubabben Sarkin Kano, garin Awe ne don zaman hijira bayan Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tube shi daga gadon sarauta.

Rahotanni daga jihar Nasarawa sun ce Sanusi II ya gabatar da Sallar Juma’a a garin Awe kamar yadda mutanen garin suka bukata.

A yayin ziyarar Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, rahoton na cewa Gwamnan da Sanusi II za su tafi Abuja inda daga nan zai kama hanyar zuwa Legas.

Hakan dai ya biyo bayan umarnin da wata babbar kotu a Abuja ta bayar na cewa a bai wa Muhammadu Sanusi damar shiga ko ina a Najeriya ban da Kano.